Main menu

Pages

BABBAN COMPANY JAKA DA NAFISA ABDULLAHI ZATA BUDE MAI SUNA NAAF LUXURY

 


Jaruma Nafisa Abdullahi zata bude babban company na jikkunan Mata'yan kwalisa

Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, za ta kaddamar da katafaren kamfanin ta na hada jakunkunan mata 'yan kwalisa Kamar yadda jarumar ta sanar a Instagram, ta fara hada jakunkunan tun wasu watanni da suka gabata amma ita ke amfani da kayan ta. A cewarta, zata kaddamar da su a ranar 14 ga watan Augusta wanda zata iya cewa yana daga cikin burikanta da ta dade tana raino.


Kamar yadda jarumar ta sanar, ta yi watanni tana amfani da jakunkunan kamfanintan amma sai yanzu ne ta ga lokaci yayi da zata tallata su ga duniya. Ga abinda Jarumar tace kamar haka;


Wani yanayi mai muhimmanci nake shiga idan na ganni ina yin abinda nake mafarki. "Daya daga cikin tsofaffin burikana shi ne in samu jakunkuna da suka fito daga gareni, in iya daukar jakar zuwa kowanne sashi na duniya dauke da sunana. 


Na samu nasarar yin hakan shekarar da ta gabata. "Eh, amma ban ji cewa wancan lokacin bane ya kamata in nunawa duniya NAAF Luxury. Bayan yin gaba da komawa baya tare da yanke hukuncin yi, zaben launikan da suka dace, na shirya gabatar muku da su duka!!!". To sai muce Allah Ya bada sa'a Ya albarkaci wannan kasuwanci.

Comments