Main menu

Pages

MU LEKA KITCHEN (FRIED COUSCOUS)


Yadda Ake yin fried couscous

INGREDIENTS;

Couscous 

Carrot

Green beans

Green piece

Tattasai

Attarugu

Oil

Albasa

Maggi

Gishiri

Spices

Hanta  or nama


METHOD

Da farko zaki fara dafa green beans ɗinki saboda yana daɗewa bai dahu ba saiki yan-yanka carrot ɗinki shima ki dafa ki saka green piece ɗinki aciki shima saiki ajiye gefe, zaki tanana hantanki kokuma nama duk abunda kike dashi har kifi zaki iya sakawa saiki ajiye gefe ki yanka albasa shima aciki. kKiɗauko tukunyarki kizuba mai(oil) kiɗan yanka albasa aciki yanda zaiyi ƙamshi saiki zuba couscous ɗinki kinata juyawa harsai yayi brown saiki juye amatsami man yaɗan tsane, kizuba mai kaɗan kisaka kayan miyanki aciki, magi, gishiri, kori da kayan Kamshi. Saiki zuba ruwa dai-dai misali a tukunya idan ya tafasa kizuba fried couscous ɗinki aciki kisa leda kowani abu kiɗan rufe couscous ɗin dashi, Daman kin rigada kin dafa su carrot dinki saiki juye couscous ɗinki acikin haɗin ki ɗan juya yanda komai zai haɗe. A ci girki Lafiya.

Comments