Main menu

Pages

AMARYA TA ZIYARCI GIDAN YARI DALILIN GWABJE UWARGIDA.

 


An Kai wata Amarya gidan yari saboda buge uwargidansa saboda shiga gidan gaba a mota

Wata amarya ta tsinci kanta a gidan yari bayan da ta sumar da kishiyarta sakamakon rubibin shiga gidan gaba a motar mijinsu.jaridar DNH na ruwaito


Lamarin ya faru ne a Jihar Kano a makon da ya gabata, bayan da uwargidan ta shaida wa Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da ke Kofar Kudun gidan sarki, ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda tai ƙorafin cewa kishiyarta ta mata duka.


A cewar mai ƙarar, ba ta da lafiya, sai mijin nasu ya aiko da mota a kai ta asibiti, sakamakon ita ba za ta iya tuƙa tata motar ba


Ta ƙara da cewa shigar ta motar ke da wuya, kwatsam sai ta ga kishiyar ta riƙe da kofar motar ta na ce mata ta fito, sai ita kuma uwargidan tace mata ba za ta fito ba saboda asibiti za a kai ta.


“Kafin ka ce kwabo, sai na ji ta doke ni a goshi na, nan na faɗi a sume, shine a ka garzaya da ni asibiti,”


Sai dai kuma amaryar ta musanta laifin na ta.

Daga nan ne sai Sarki Yola ya sa a ka aike da ita zuwa gidan yari zuwa mako mai zuwa domin ci gaba da shari’ar.


To wait me yayi zafi haka, ga dukkan alamu dai ita wannan Amarya fitinanniyace Kuma bakuwar shiga mota, in ba haka ba me yayi zafi haka. To lah Ya kyauta Ya sa mufi karfin zukatanmu Ameen.

Comments