Main menu

Pages

ABUBUWA 7 DA YA KAMATA KU SANI GAME DA RANA

 Abu bakwai da kuke bukatar sani game da rana


Wataƙila mutane da yawa sun zaci a yadda suke hango rana a sama to haka take a zahiri, wasu ma a tunaninsu jirgin sama kan wuce ta idan ya tashi.


Sai dai duk ba haka lamarin yake ba, rana da ake gani tana fitowa da faɗuwa tana tattare da wasu bayanai masu ban al'ajabi da wataƙila ba ku taɓa sani ba.


Mutane da dama sun yi amannar cewa rana fitowa take yi tana faɗuwa, wato wayewar gari da kuma dare kenan.


Amma a zahiri sai dai a ce rana kan ɓullo ne a ɓangaren da gari ya waye, wato idan duniyarmu ta Earth ta juya gefen da ranar take, to sai ta ɓullo a ganta a wannan yanki.Idan kuma duniyar ta sake juyawa ɗaya ɓangaren, sai a ga duhu kamar yadda ainihin sararin samaniyar yake.


A wannan maƙalar, mun yi duba ne kan rana da bayanan da suka shafe ta da kuma amfaninta ga rayuwar ɗan adam kamar yadda Allah Ya tsara.


Mece ce rana?

Rana siffarta tamkar ƙwallo take, tana ƙunshe da iskar hydrogen da helium, kuma masana kimiyya na hasashen ta samu ne shekara biliyan 4 da miliyan 500 da suka wuce.


Kuma hasken rana da muke samu a duniyarmu ta Earth, shi ne jigon tafiyar da rayuwar mutane da dabbobi da duk wasu halittu da ke rayuwar a duniyarmu ta Earth.


Wato ma'ana dai, ita ce ke ciyar da rayuwarmu da dukkan abubuwan da Allah Ya halitta a ƙarƙashinta.


Asalinta kuma, hasashen kimiyya ya nuna ta samu ne ta yadda fashe-fashen nukiliya a tumbinta suka amayo da ƙwayoyin halitta, waɗanda suka yi ta maƙaluwa suna goyon juna ta hanyoyi iri-iri, har sai da halittu suka tsiro daga gare su, kamar yadda marigayi Bashir Othman Tofa ya rubuta a littafinsa na Kimiyyar Sararin Samaniya.


Akwai duniyoyi tara da suke zagaye rana a unguwar tamu ta Solar System, sannan akwai dubun-dubatar curarrun duwatsu masu zagaya rana cikin ƙwambarsu da aka fi sani da asteroids, da kuma comets har tiriliyan uku da ke zagaye ta.


Comets wata curarrar aba ce mai kan ƙanƙara amma kuma tana feshin gas da ƙura, da suke ziyartar unguwar rana su zagaya su koma.

Comments