Main menu

Pages

YADDA WASU MANIYYATA SUKA FADA HANNUN DAN DAMFARA A NIGERIA

 



Yadda aka damfari wasu maniyyatan Hajj. Niger state

Hukumar alhazai ta jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta ce akwai gwamman maniyyata na wannan shekarar wadanda ba za a yi hajjin da su ba sakamakon fadawa hannun wani dan damfara.



Maniyyatan sun shiga wannan halin ne bayan da suka ce sun biya wani jami’in hukumar kula da alhazai ta jihar kudinsu na sauke farali, sai dai hukumar ta ce ba a saka kudin a asusunta ba.



Bayanai sun ce maniyyatan da lamarin ya rutsa da su sun kai kimanin dari da hamsin.


Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa a karamar hukumar Bida ta ce ta yi burin gudanar da aikin Hajjin a bana kuma tun shekaru biyun da suka gabata ta fara biyan kudin amma saboda cutar korona hakan bai yiwu ba.


 

Ta ce “Ban sani ba, ina ta wahala muna yin training, muna yin komai tare da su amma jami’in da muka bai wa kudi bai fada mana cewa bai biya kudin ba.”


 

Ta kara da cewa tun da ta samu labarin cewa kudinta ba su isa wurin hukumomi ba take fama da rashin lafiya saboda girgiza ta da labarin ya yi.



Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja ta tabbatar da cewa ta samu irin wadannan korafe-korafe.


Ta kuma ce ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya faru bayan wasu maniyyata sun yi ikirarin cewa sun biya kudinsu ga wani jami’inta.


 

Shugaban hukumar, Alhaji Umar Maku Lapai, ya ce sun umarci shugaban karamar hukumar Bida ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike.



Ya kuma ce ba za su iya daukar wani mataki ba sai an ga abin da bincike ya nuna.

Sai dai ya kara da cewa yanzu haka jami’in da ake zargin yana hannun jami’an tsaro.

Ana sa ran rahoton binciken ya fito nan ba da jimawa ba.

Comments