Main menu

Pages

TUDU BIYU; UBA SANI YA ZABI HADIZA BALARABE MATSAYIN MATAIMAKIYA,

 Yadda Uba Sani ya Kara zabar Hadiza Balarabe matsayin Mataimakiya, a zaben bana

Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya zaɓi mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyar gwamna a zaben 2023.A sanarwar haka da ya fitar da kansa, sanata Uba ya ce bayan ganawa da tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki suka yi na jam’iyyar, ya amince ya zaɓi Balarabe a matsayin mataimakiyar gwamna a zaben da ke tafe a 2023.


” Ina so in sanar muku cewa na zaɓi Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyar gwamna.


” Hadiza Balarabe jajirtacciyar ma’aikaciyace kuma ta bada muhimmiyar gudunmawa a nasarorin da gwamna Nasir El-Rufai ya samu a jihar Kaduna.


” A dalilin haka ya sa nake kira a gare ku da ku mara min da ita baya domin samun nasara a zaɓen da tafe da kuma cigaba da Kwankwaɗan romon dimokuraɗiyya a jihar Kaduna.


Sanata Sani ne ke wakilta Kaduna Ta Tsakiya a majalisar dattawa.


Mohammed Dattijo ne ke yin takarar kujerar sanata a zaɓen dake tafe.


Wannan shine karo na biyu da za ayi takara na Musulmi gwamna, mataimaki ko mataimakiya gwamna.


Gwamna El-Rufai ne ya maye gurbin bar Anas Bantex da Hadiza Balarabe a zaben 2019, bayan tsohon mataimakin nasa, Bantex ya koma takarar sanata a yankin Kaduna ta Yamma.


Sanata Danjuma Laah yayi nasara a zaɓen a 2019.

Comments