Main menu

Pages

ENGLAND ZA TAYI RAM DA WANI LIKITA DAN NIGERIA

 England zata kwamushe Wani doctor Dan Nigeria

Mai gabatar da kara a kotun Sarauniya da ke Manchester, a Ingila ya shaidawa kotu cewa, wani likita ya kashe wata mata, uwa, da ta je asibiti a duba lafiyarta, sakamakon kauce wa wata ƙa'ida da ya yi.An shaida wa kotun cewa Dakta Isyaka Mamman, mai shekara 85, ya aikata abubuwa da dama da suka saba ƙa'ida, kafin wannan abin da ya kai ga mutuwar matar.Tun a baya daman hukumar da ke kula da likitoci ta taba korar Dakta Mamman, wanda ya amince da aikata kuskuren da ya yi sanadiyyar mutuwar matar, saboda karya da ya yi a kan yawan shekarunsa na haihuwa.


Amma kuma bayan wani lokaci aka sake daukarsa aiki a asibitin Royal Oldham Hospital.A ranar Talata ne kotu za ta yanke masa hukunci a kan samunsa da laifin sakaci da aiki da ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata mai 'ya'ya uku.Shahida Parveen, mai shekara 48, ta je asibiti ne a ranar 3 ga watan Satumba, 2018, tare da mijinta, domin gudanar da bincike kan yadda jikinta ke samar da jini da yawa fiye da ƙa'ida.A dalilin haka ne aka bayar da shawara kan a yi mata wani bincike a cikin bargonta, kamar yadda mai gabatar da kara, Andrew Thomas QC, ya gaya wa kotu.A ƙa'ida ana debo ɓargo ne daga ƙashin ƙugun mutum, maimakon haka sai Mamman, bai yi hakan ba, da farko, in ji mai gabatar da karar.Maimakon hakan sai likitan ya bi hanyar da ba a saba bi ba, kuma mai haɗarin gaske.


Inda ya yi kokarin samo ɓargon daga ƙashin ƙirji ko nonon matar, duk da cewa matar da mijinta sun nuna rashin amincewarsu, kamar yadda aka shaida wa kotun.Bugu da ƙari likitan ya kuma yi amfani da allurar da ba ta dace ba, wajen ɗebo ɓargon, wanda a kan haka ya kuskure ƙashin, allurar ta huda jakar da zuciyarta ke ciki, hakan kuma ya sa ta yi ta zubar da jini a cikinta.Ms Parveen ta suma daga lokacin da allurar ta huda jakar zuciyar, kuma ba ta kwana ba a wannan rana, rai ya yi halinsa.


Shi dai Mamman ya zama likita ne a Najeriya tun a shekarar 1965, kuma yana aiki a Birtaniya tun 1991.


Tun daga 2004 har zuwa lokacin da ya samu wannan kuskuren yana aiki ne da asibitin Pennine Acute Hospitals.Haka kuma an gaya wa kotun cewa batun shekarunsa na haihuwa ma, wani abu ne da aka taba samun ce-ce-ku-ce a kansa, saboda inda aka haife shi a Najeriya, ba a rijistar haihuwa a lokacin.Da farko dai ya gaya wa Ma'aikatar lafiya ta Birtaniya cewa an haife shi ne a 1941, amma kuma daga baya ya ce a 1947, ne abin da ke nuna cewa ya fara karatunsa na digiri a shekara goma kenan.A 2004 hukumar kula da likitoci ta Birtaniya ta same shi da saba ƙa'idar aiki abin da ya sa ta dakatar da shi tsawon shekara daya, saboda karya a kan shekarunsa.


Hukumar ta sallame shi amma kuma ta sake ɗaukarsa aiki a 2006, bayan an tsayar da magana cewa an haife shi ne a 1943.Mamman ya bar aikinsa da Medway Trust saboda matsalolin rashin ƙwazo, kuma a shekara ta 2015 an gabatar da ƙorafi ga asibitin Oldham da yake aiki.


An yi hakan ne lokacin da wani maras lafiya ya ce an yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima a lokacin ɗiban ɓargonsa domin gudanar da bincike.Haka kuma a dai wannan shekara an sake samun wata matsalar ta ɗiban ɓargon, inda aka yi wa maras lafiyar allura a wurin da bai kamata ba.


Maras lafiyar ya tsira, bai mutu ba, amma kuma ya samu nakasa ta dindindin.

Comments