Main menu

Pages

SUBHANALLAH, WANI MAIGADI YA HAU DOKIN ZUCIYA, TA KAISHI TA BARO

 Yadda Wani Maigadi ya hau Dokin zuciya 

Wani magidanci ne ya daka ta zuciya ya aikata barambarama. Shi dai wannan maigadi ya shiga hidimar da babu ruwansa ne shiyasa abin ya bashi Ruwa.A yadda ya bada labari dakansa lokacin da yake a hannun hukuma sannan da manema Labarai. Ya bada labarin ne kamar haka.Da farko dai yace shi maigadi ne a Wani gida, to ana haka sai wata rana yaji wata makociyarsu inda yake gadin ya ringajin ita wannan Mata tana yi da matar gidan da yake gadin.Tana cewa wance bata da zumunci bata shiga sabgar kowa irin dai 'yan gulmace gulmace na unguwa. To lokacin da wannan Maigadi yaji ita wannan Mata tana yawan gulmar uwar dakinsa, wato matar mutumin da yake ma gadi.Sai ya tunkareta kai tsaye yace Mata don me za ta dinga gulmar matar gidan da yake gadi. To shi Kuma ana shi ganin wata kila ya Isa da itane Kuma ya Isa ya gaya Mata gaskiya, saboda baba ma take kiranshi dashi saboda sunan babanta gareshi. Wata kila hakan ne ya bashi karfin gwiwar tunkarar ta da wannan zance.Inda Akai rashin sa'a ita Kuma abin bai Mata dadi ba sai ta hau zaginshi tana ce Mai Mai matattar zuciya bai iya aikin komai ba sai gadi, Jahilai da kiki da sauran bakaken maganganu duk ta gaya mai tayi tafiyar ta gida.
To ashe shi Kuma abin bai mashi dadi ba hasali ma maganar ta tsaya Mai a wuya taki wucewa. A ranar cikin dare misalin karfe 2:00am ya tasamma gidan wannan Mata.Yayi sa'a ya shiga cikin gidan Kai tsaye ya tunkari dakinta hannunsa dauke da adda. Ko da ya shiga ya gasnhi sai ta tashi tana cewa me Kuma ya kawo ka gidana.Shi Kuma bai yi wata wata ba sai ya hau saranta da adda, Amma a cewarsa bai San wajen kaifin ne ya sa ba. Bayan yayi Mata sara hudu, ya juya zai tafi sai 'yar diyarta ta farka ta Kuma kama sunanshi, ganin haka nan ma bai Jira komai ba ya dauki 'yar yarinyar ya dankara kanta a saman tiles, nan take tabi uwarta lahira.
Amma yace gudun kar asirinsa ya tonu ne yasa ya kashe yarinyar ganin ta gane shi.
T a nan meye hadin shi da shiga sabgar Mata, Ina ruwanshi da wadda Ake zagin, Kuma ita waccan da ya kashe ai tana da Miji Mai yasa da yayi Mata magana ta zazzageshi bai kai kararata wajen mijin ba sai ya dauki doka a hannunsa ya kashe ta.To Jama'a ya kamata mu hankalta mu daina shiga sha'anin da baby ruwanmu a ciki. Sannan mu guji Hawa Dokin zuciya don ba inda zata kaimu sai tashar dana sani.


Comments