Main menu

Pages

SAFA - SAFARA'U, NA CIKIN MAWUYACIN HALIN DA TAKE BUKATAR ADDU'A




 Mu Tausayawa Safara'u A Matsayin Ta Na `Yar Uwar Mu Musulma


Tabbas akwai abun ban takaici da bakin ciki mai cike da dacin zuciya a ce kaga musulmi ko musulma suna kokarin zama ribar shedan a nan doran duniya.



Abun ban takaicin ma shine irin yadda harkar fina finan hausa ta lalata tarbiyar wasu `ya`yan musulmai kuma hausa fulani irin su Safara'u  da dai sauran ire - iran su.



Ya zama dole akan mu musulmai mu tausayawa duk wanda muka ganshi a cikin wani yanayi wanda yaci karo da koyarwar addinin Musulunci badon komai ba sai dan kallan yadda makomar shi zata kasance idan har ya koma ga Allah a haka.



Duk wanda yasan Safara'un da ta cikin kwana Casa'in yaga wannan yasan ba ita bace, bata cikin hankkainta, bata cikin hayyacinta Kuma kamanninta sun sauya akan yadda take a da.



Hatta wasan da suka he Nijer sukayi da sallan nan duk Wanda yaga rawar batsar da Safara'un tayi tare da ubangidan ta Mr 442 sai abin ya bashi haushi da takaici. 



Kuma ni a nawa ganin ba wai fina finan Hausa ne kawai ke taka rawa wajen bata tarbiyya ba, a'a har da iyaye. Muna fatan Allah Ya shiryeta da ita da duk Wani Musulmi da shaidan ke rudar sa. Allah Ya sa su gane su dawo hanya tun kafin lokaci ya kure masu. 

Muna rokon Allah ya shiryar da Safara'u da mu baki daya.





Allah Ya shiryeki Ya shiryar damu baki daya.

Comments