Main menu

Pages

SARAKUNA 8 DA AKA DAKATAR SBD ZARGIN SUNA TARE DA 'YAN FASHIN DAJI

 


An sauke Sarakuna Takwas Bisa Zargin da ake masu

ranar Lahadi ne gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta dakatar da Sarkin Birnin 'Yandoton Tsafe sakamakon nada wani mutum da ake zargi da zama kasurgumin dan fashin daji a matsayin Sarkin Fulanin yankin.


Sarkin Birnin 'Yandoton Tsafe ya nada Adamu Aliero a sarautar Sarkin Fulani ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a karshen makon jiya.


Wasu rahotanni sun ce jami'an gwamnati na cikin wadanda suka halarci bikin nadin sarautar.


Sai dai gwamnatin Jihar ta Zamfara ta nesanta kanta daga nadin Aliero tana mai cewa hakan bai dace ba.


'Yan-sanda a Jihar Katsina da ke makwabtaka da Zamfara sun ce har yanzu suna neman Adamu Aliero ruwa-ajallo bisa hannu a kashe mutane da dama.


Mai magana da yawun rundunar 'yan-sandan Jihar, SP Gambo Isa, ya shaida wa BBC Hausa cewa "Adamu Aliero na daga cikin masu kashe mutane da kama mutane su yi garkuwa da su, kuma muna nemansa a kan ta'addancin da ya aikata a garin Kadisau, inda ya kashe sama da mutum ɗari."


Dama an dade ana zargin wasu sarakuna da taimaka wa ‘yan fashin daji wurin aiwatar da ta’asar da suke yi, inda aka sauke wasu daga kan mukamansu.


Gwamnatocin Jihohin Katsina da Zamfara ne a kan gaba wajen dakatar da sarakunan.


Baya ga Sarkin Birnin 'Yandoton Tsafe, ga jerin sarakunan da aka dakatar kan zargin alaƙa da ƴan fashi:



Sarkin Zurmi

Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar na cikin sarakunan da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar kan zargin alaƙa da kashe-kashen da 'yan fashin daji ke yi a yankin masarautarsa.


Gwamnatin jihar ta ce Gwamna Bello Matawalle ya kafa kwamatin bincike ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken.


An umarci Bunun Kanwa, Bello Suleiman, da ya karɓi jagorancin masarautar nan take.


Dakatar da Sarkin Zurmin na zuwa bayan harin da aka kai a ƙauyen Kadawa da ke cikin mulkinsa inda rahotanni suka ce an kashe kusan mutum 100.



Sarkin Dansadau

Sarkin Dansadau, Hussaini Umar na cikin sarakunan da aka dakatar a jihar ta Zamfara. A ranar 1 ga watan Yuni gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin kan zargin alaƙa da 'yan fashi. Dagacin Dansadau Nasiru Muhammad Sarkin Kudu ya karɓi ragamar masarautar. Haka kuma Gwamna Matawalle ya kafa wani kwamati da zai binciki sarkin kan zargin da ake masa, ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin sufetun ƴan sandan Najeriya DIG Mohammad Ibrahim Tsafe (mai ritaya)



Sarkin Maru

Sarkin Maru ne basarake na farko da gwamnatin PDP a Zamfara ta fara dakatarwa tare da tuɓe shi kan zargin hannu a matsalar tsaron jihar.


A watan Agustan 2019 gwamnatin Matawalle ta tsige Sarkin Maru Abubakar Chika bisa zargin cin amanar talakawansa kan alaƙarsa da ƴan bindiga masu kashewa da satar mutane.


Gwamnatin Zamfara ta ce ta tsige Sarkin na Maru ne bayan da kwamitin da ta kafa na binciken zarge-zargen hannun sarakunan gargajiya a sata da garkuwa da mutane, ya samu Sarkin 'da hannu dumu-dumu'.


Gwamnatin ta fara dakatar da basaraken ne kan zarginsa da wasu talakawansa suka yi yana da alaka da masu satar jama'a.


Sai dai ɓangaren sarkin na Maru ya musanta zarge-zargen da ake yi wa basaraken.


Baya ga sarakuna akwai kuma wasu hakimai ko dakatai da aka dakatar waɗanda ake zarginsu da alaƙa da ƴan bindiga.


Dagacin garin Kanoma

Dagacin garin Kanoma a ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, Alhaji Lawal Ahmad shi ma an dakatar da shi kan zargin alaka da masu sata da garkuwa da jama'a.


Gwamnatin Zamfara ta dakatar da shi ne tare da Sarkin Maru Abubakar Chika a 2019.


Kwamitin amintattu karkashin jagorancin tsohon sufeto janar na 'yan sanda, Muhammad Abubakar ne ya bayar da shawarar dakatar da hakimin.


Kwamitin ya ce bincikensa ya gano yadda masu garkuwa da jama'a ke amfani da sarkin Maru da kuma hakimin Kanoma wajen biyan kudin fansa.



Dagacin Nasarawa Mailayi

An dakatar da Dagacin Nasarawa Mailayi, Bello Kiyawa, tare da sarkin Zurmi saboda zarginsa da alaƙa da ƴan fashin daji.


Gwamnati ta zargi hakimin da haɗa baki da ƴan fashin daji masu addabar jihar.


Yankin Zurmi da ke makwabtaka da Katsina ya daɗe yana fama da hare-haren ƴan fashi masu satar shanu da mutane.



Sarkin Yakin Kanwa da Marafan Bakura

A watan Janairun 2020 ne gwamnatin Zamfara ta dakatar da wasu uwayen ƙasa guda biyu da ke ƙananan hukumomin Bakura da Zurmi.


Gwamnatin ta dakatar da Alhaji Bello Garba Kanwa, Sarkin Yakin Kanwa da kuma da kuma Alhaji Muhammad Bello Yusuf wanda shi ne Marafan Bakura.


Gwamnatin Zamfara ta ce ta dakatar da uwayen kasar biyu ne bisa rashin biyayya da kuma karan tsaye ga shirye-shiryen gwamnati.


Sauran laifukan sun hada da shiga dumu-dumu cikin harkokin siyasa da kuma zargin almundahana da ruf da da ciki da dukiyar al'umma.


To amma da yawa na ganin takun saka tsakanin sarakunan da kuma gwamnatin jihar ba ya rasa nasaba da siyasa.


Kuma wannan ya fara tun lokacin da uwayen kasar suka karbi belin wasu tsoffin kwamishinoni a bangaren jam'iyyar adawa ta APC da gwamnatin Bello Matawalle ta tsare bisa wasu zarge-zarge.


A hira da BBC a farkon mako Yusuf Abubakar Zugu ya musanta cewa akwai siyasa cikin dakatar da sarakunan.


Amma jam'iyyar adawa ta APC ko a baya ta fitar da sanarwar cewa ƴaƴanta a jihar Zamfara na fuskantar takura daga gwamnatin PDP mai ci, wani abu da gwamnatin ke musantawa.



Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara

watan Mayun 2021 ne masarautar Katsina ta dakatar da hakimi kan matsalar tsaron jihar.


An dakatar da Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, bisa zargin da ake yi masa na alaka da 'yan fashin daji da suka addabi jihar Katsina.


Masarautar Katsina ta ce ta dauki wannan mataki ne domin jaddada wa gwamnati da al'umma cewa tana goyon bayan yaki da ta'addanci da mahukunta ke yi.


Tuni masarautar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa hakimin na Fawwa Alhaji Abubakar Yusuf.


Wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa sun hada da hada baki da yan sa kai wajen aikata wasu abubuwa da ba a fito fili an bayyana ba.


Alhaji Mamman Iso, Sarkin Yakin Katsina, kuma sakataren masarautar Katsina, ya shaida wa BBC cewa babu kanshin gaskiya a zargin da wasu ke yi na cewa ana yi wa hakimin bi ta da kulli ne.


Ya ce idan kwamitin da aka kafa ya kammala bincike zai gabatar da rahotonsa wanda za a aika wa gwamnati, sannan idan har an gano cewa bai aikata laifin komai ba za a bayar da umarnin mayar da shi kan kujerarsa nan take.

Comments