Main menu

Pages

CIKAKKEN SHARHI AKAN FILM DIN IZZAR SO

 Tsokaci akan film din Izzar So

Assalamu alaikum Warahmatullah. A yau post din namu zamu karkata ne wajen yin sharhi akan fitaccen Shirin film din nan na Izzar So, film Mai dogon zango.
Wannan film kwarai yana taka Muhimmiyar rawa wajen koyar da darussa kala - kala. MUSAMMAN ma ta fuskar addinin Musulunci. Kwarai dagske wannan film Yana fadakarwa da tunatar da Musulmai abubuwa da dama akan addini.
Sannan Jigon film din shine riko da gaskiya da Amana, wannan ba karamin al'amari bane. Sannan an nuna yadda gaskiyar da rikonbamana ke rinjaye akan dukkan Wani sharri ko tuggu da za ayi Mai Mai wadannan halayya.
Farkon Shirin Izzar So, an nuna tsantsar Izza ta mulki da Isa. Sannan a tsakiyan Shirin film din Kuma sai aka nuna Izza ta gadara da tuggu da BITA da kulli. A yanzu Kuma sai Ake fafatawa tsakanin karya da gaskiya inda gaskiyar dai a kullum itace a sama.
To wai Ina da tambaya, shi wannan film wane suna yafi dacewa a kiranshi da shi. Ance Mai izzar So, Kuma gashi soyayyar dake cikin film din ko kwata bata Kai ba balle a kira ta da rabi. Cakusawa kawai akeyi. Kuma a yanzu anzo Gabar da abun yayi zafi yayi tsamari sosai. To maji Kuma ma gani, shin ya zata kwaranyene.


Comments