Main menu

Pages

KALLO YA KOMA SAMA; OBASANJO NA KABU -KABU DA NAPEP A OGUNYadda Obasanjo ya dinga daukar fasinja a Keke Napep

 Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya karaɗe wasu titinan birnin Abeokuta ya na ɗauka da sauke fasinja a cikin babur ɗin Keke NAPEP, wato A Daidaita Sahu.


Obasanjo ya yi ɗaukar fasinjojin ne a ranar Asabar ɗin nan, domin murnar cikar sa shekaru 85 a duniya.

An haifi Obasanjo a ranar 5 Ga Maris, 1937.Obasanjo wanda aka fi kira Baba ko OBJ a yanzu, ya fara tuƙa Keke NAPEP ne daga farkon Titin Mashood Abiola har ƙarshen sa daidai babban gidan mai na NNPC ‘Mega Station’.

Sannan kuma ya riƙa ɗaukar fasinja ya na saukewa inda ya lula kan hanyar Kasuwar Kuto.Baba wanda ke sanye da kayan gargajiya na Yarabawa da kuma hula hana-sallah, ya ja hankalin mutane da dama, inda aka riƙa rububin shiga, har ana bin sa a guje domin a samu ‘tubarrakin’ hawa mota mai babban direba da ba a taɓa samun direba irin sa ba.Idan ba a manta ta ba, cikin wannan makon ne Obasanjo ya raba wa matasa Keke NAPEP 85 domin murnar cikar sa shekaru 85 da haihuwa.
Comments