Main menu

Pages


Falalar yin Istigfari

 Ayoyin Kur’ani da Hadisan manzon Allah SAW da yawa sun bayyana falalar yawaita neman gafara daga wurin Allah Madaukakin Sarki.


Neman yafiyar Allah da tuba bisa laifukan da bawa ke yi yana da tasiri a rayuwar bawa ta yau da gobe kamar yadda Alkur’ani mai tsarki ya kawo a wurare da dama.



Yadda bakuwar cutar tumatir ke jawo wa manoma asara a Filato

Karuwai sun lakada wa matar aure duka a gaban mijinta

Manzannin Allah gaba daya sun kira al’ummominsu da su kasance sun­ yawaita ambaton Allah tare da neman afuwa da kuma neman yardarSa.



Cikin Alkur’ani Allah SWT ya ce, mu nemi gafararSa Shi kuma zai gafarta mana. Bugu da kari Zai yalwata mana arziki da samar mana da jin dadin duniya da na lahira.



An ruwaito ciki hadisi cewar Manzon Allah yakan yi istigfari a rana sama da sau 70, a matsayinsa na Annabi da Allah ya tabbatar masa da yafiya da kuma yardarsa.


Falalar yawaita istighfari sun hadar da:

- Kankare zunubai

- Yalwar arziki da dukiya

- Samun haihuwa da yawan ’ya’ya

- Samun nutsuwar zuciya

- Samun damina mai albarka

- Saukaka alamarin bawa a rayuwarsa

- Bawa zai samu rabaita da gidan Aljanna


Wani babban malami ya ce babu wata damuwa ko matsala da ya taba shiga face ya tunkare ta da yawan neman gafarar Allah kuma cikin ikonSa Yana kawo masa sauki.

Comments