Main menu

Pages

FALALAR NAFILA KAFIN ZUHR DA KUMA KAFIN ASR

 


Falalar Nafila, kafin Sallar Zuhr da Kuma kafin Asr

Assalamu alaikum Warahmatullah. A yau mun zo maku da wata ibadah Mai matukar falala, wadda Annabi Muhammad SAW yace, duk wanda ya lazimci yinsu a kullum to kuwa wuta ba zata taba cin namansa ba Insha Allah.Wannan Ibadah kuwa ita ce, yin Nafila raka'a hudu,( ayi biyu a sallame a Kara wasu biyun ayi sallama) kafin Sallar Zuhr, WAYO Azahar a Hausance. Da Kuma yin raka'a hudu bayan Sallar Azahar din. Kun ga ya zama hudu kafin Azahar hudu kafin La'asar wato Asr.Wata ruwayar Kuma har ila yau, Annabi Muhammad SAW yace Rahmar Allah ta tabbata ga duk Wanda ya lazimci yin Nafila raka'a hudu kafin Sallar La'asar.Don haka sai mu dage don mu samu tsira daga wutar jahannama da Kuma kasancewa cikin rahamar Allah Duniya da Lahira. Allah Ya bamu ikonyi Ameen Ameen.

Comments