Main menu

Pages

FALALA DA AMFANIN DA NAFILA ZA TAYI MA MUTUM RANAR LAHIRA

 


Amfanin da Nafila za tayi ma Bawa ranar Lahira

A ranar Lahira Allah SWT Zai umarci mala'iku da sun binciki Sallar Bawa. Idan aka duba aka ga bata cika ba, za su fada ma Ubangiji cewa Sallar wannan Bawa akwai tasgaro bata cika ba. Duk da kuwa Allah Ya fisu sani.
To a nan sai Allah Ya ce a duba a gani idan yana da sallolin Nafila, idan aka duba aka ga akwai sai Allah Ya ce a cike inda Sallar farillar Bawa ke da tasgaro da sallolin Nafila.

Nan take mala'iku zasu duba idan akwai acike ma mutum dasu shikenan sai ace ya wuce, Allah Ya taimakedhi ya tsallake.
Amma fa idan babu Sallar Nafila to shikenan ya samu matsala, ba Kuma zai samu damar wucewa ba. Allah Ka bamu ikon yawaita sallolin Nafila.Comments