Main menu

Pages

AN KAWO KARSHEN ZAWARCIN CHRISTIANO RONALDO

 



Chelsea ta kawo karshen neman daukar dan kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo.


Dan wasan tawagar Portugal, mai shekara 37, na son barin United, wanda ake alakanta shi da zai koma Stamford Bridge.


Sai dai kuma bayan da Chelsea ta kammala sayen Raheem Sterling ranar Laraba, Thomas Tuchel ya ce ya mayar da hankali wajen daukar masu tsaron baya.


Shi kansa kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce Ronaldo yana cikin 'yan wasan da yake bukata a bana, ba za su sayar da shi ba.


Har yanzu Ronaldo bai bi United wasannin atisayen tunkarar kakar bana da take yi a Asia da Australia ba, inda Ten Hag ya ce saboda dalilin da ya shafi iyalinsa.



Mahukuntan Chelsea na cike da farincikin sayen Sterling, wanda suke hasashen ribar kafa ce ga kungiyar.


Kawo yanzu Sterling yana tare da 'yan wasan Chelsea a birnin Los Angeles a Amurka, inda take wasannin atisayenta.


Tuchel ya ce yana fatan Sterling zai taimaka wajen bunkasa kungiyar, zai kuma taimakawa matasanta da ke gurbin cin kwallaye, bayan da Romelu Lukaku ya koma Inter Milan domin buga wasannin aro.


Kociyan Chelsea dan kasar Jamus ya fada cewar ya kamata kungiyar ta yi hanzari a kasuwar cinikin 'yan kwallo, domin yin kafada da kafada da takwarorinta, bayan da aka dora mata takunkumi.


Tuni dai kungiyar Stamford Bridge ke fatan kammala cinikin Kalidou Koulibaly daga Napoli da kuma dan wasan Manchester City, Nathan Ake.


Ana kuma alakanta kungiyar da cewar tana son daukar dan wasan Paris St-Germain, Presnel Kimpembe, wanda ya yi aiki da Tuchel a kungiyar Faransa daga 2018 zuwa 2020.

Comments