Main menu

Pages

YANDA ZAKA SA WAYARKA DA TA BACE YIN RINGING KO DA AN SANYA TA A SILENT.

 Yadda zaka sa wayar ka da ta bace yin kara idan ankira ko tana silent.

Tabbas a lokutta da yawa a wajen taron bukukuwa mutum zai Jira hannu a aljihu don dauko wayarsa Amma sai yaji bata nan, ko kuma mata su ajiye jakarsu don zuwa yin Wani uzuri kafin su dawo an bude jaka an dauke waya.Hakan kuwa yana tayarwa Mai wayar hankali sosai da tunanin ta Ina zai fara neman wayar.Wani lokacin kuma ba dauke wayar akayi ba misali ace a gida waya na iya fadawa wani wurin ko tsanin kujeru ko bayan Wani abu Azo ayi ta nema ba a gani ba. To ga yadda za ayi a gano ta.
Akwai wani application find my device da zai bada damar gano inda take ta hanyar amfani da GPS sannan kuma da yin kara wato ring. Sai dai kuma idan fa baka da wata wayar ko computer ko wata na'uran da za a iya amfani da wannan app din to hakan fa ba zai yuwu ka gano wayarka ba.But idan a gida kuke sai ka amfani da wayar Wani daga cikin family member idan a wajen Biki ne sai a ari wayar aboki ko kawa.
Idan ka amshi wayar sai ayi installing app din a wayar sai kasa login credentials dinka na google account dinka. Idan kana tunanin a wajen ne wani ya satar ma waya to nan take zaka kama shi read - handed,Da farko dai za kai download din Find My Device app daga Google Play Store.


Bayan angama installing, sai a bude app din wanda aka satar ma waya ya sanya email and password na google account dinshi. 


To da an sanya to duk wata wayar dake dauke da wannan google account zata bayyana. To sai ka danna daya daga cikin devices din zaka ga sound option a can kasa to sai ka danna shi.


To daga nan wayar zata fara ringing ko a Ina take, Kuma koda tana cikin silent kuwa

Comments