Main menu

Pages

KO KUNSAN WADDA KE YIMA MAWAKI WIZKID KWALLIYA, 'YAR AREWA CE KUMA MUSULMA.

 Zainab Dake Zaune A London tace bata boye cewa ita Musulma ce.


Abin mamaki shine wata matashiyar Budurwa Mai suna Zainab Hassan wadda take yi ma shaharren mawakin nan  Wizkid Kwalliya, tace tun tana yarinya take Sha'awar yin make up, sai gashi Allah Ya taimaketa ta shahara ta wannan fanni domin kuwa bawai Wizkid din ne kawai take ma aikin Kwalliya ba.
Akwai kamfanini manya manya irinsu NIKE, da sauransu da tayi aiki dasu Kuma tana modeling gyaran jiki da sauransu har ma aikata gareta Kuma fa duk a can London din.
Sannan abin burgewa shine tace a duk inda ta shiga bata boye cewa ita Musulma ce. Kunga kenan 'yan Arewa ku daina Maida kanku baya. Yanzu dai bari nasa maku video ku kalla kuji daga bakinta.

Comments