Main menu

Pages

KASASHE 10 DA 'YAN NIGERIA ZASU IYA ZUWA A MOTA BA SAI A JIRGI BA

 



Kasashen da Yan Nigeria zasu iya Zuwa a mota

1. REPUBLIC OF BENIN;

Idan zakaje Cotounou da sauran birane na cikin Jamhuriyar Benin to Lafiya Lau ne don kullum ana hada hada tsakanin Nigeria da Benin. Matafiya 'yan Nigeria suna rsallaka border kowane minti ko dakiqa, daga kowane sashe na kasar nan kudu maso yamma Zuwa arewacin jahohi, suna amfani ne da hanya ta kasa wajen zirga zirgansu. Su tsallaka inda suke so, duk da dai ya danganta daga Ina ka taso, but Lagos, Kano, Sokoto zaka iya samun motar haha da zata kaika Kai tsaye Zuwa Jamhuriyar Benin ba tare da wata wahala ba, kuma cikin farashi Mai sauki.




2. TOGO;

Ana dauke hanya daga Lagos abi bypass ta Cotonou to zaka ganka a Lome, saboda doguwar tafiyan Traders din Nigeria sun Fi son suje su sayo kayayyaki a Togo akan Benin, saboda su Togo harajinsu bai kai na Benin ba suna harajinsu is very low. Tashar motar Mett at Mile Two dake Lagos in kaje zaka samu abin hawa har Lome dake kasar Togo.




3. GHANA;

Tunda dadewa 'yan Nigeria suke zuwa Ghana Kuma mafi yawan 'yan Nigeria suna zuwa Ghana ne ta hanyar road transport ba tare da wata matsala ba. Saboda yanayin kasuwanci da sauran abubuwa da kansa 'yan Nigeria yawan zuwa Ghana yasa baza ka iya tsaida hanyar da suke bi wajen Zuwa can din ba amma akwai luxurious buses dake biyowa ta Lagos da Accra a kullum.




4. COTE D'IVOIRE

Kafin air transport, wato jirgin sama ya zo 'yan Nigeria da dama suna tafiya ne ta hanya wato road transport. zuwa Abidjan babban birnin Ivory coast. Garin da ke ciki na kudu maso yamma ana kiranshi garin Ejigbo suna da hadaddun motoci da akayi don passengers da zasuje Abidjan. 




5. BURKINA FASO

Tafiya daga Lagos zuwa Ouagadougou da sauran birane na kasar Burkina Faso zai fi sauki da Kuma sauri idan kaje a motar gida.



Ko Yaya dai tunda mafi yawan matafiyan sun Fi amfani da motar haya connection mafi kyau shine ace kodai daga Ivory coast kake zakabi ta arewacin Ghana, zuwa Ouagadougou daga Ghana an fi sanin ta nan wajen yanzu.




6. LIBERIA;

Duba da fadan farar Hula a Liberia da shigar cikin abin da Nigeria tayi 'yan kasuwa da dama sunyi tafiya ta mota zuwa kasar don shigo da wasu abubuwa da ake bukata ga 'yan Laberian wadanda abin ya shafa. (Yakin). Bayan road transport ya zama sanannen abu Kuma an saba dashi. Yanzu haka zaka samu motar haya daga Lagos direct zuwa Monrovia kullum. Mafi yawancin masu tafiya 'yan kasuwa to ta hanya suke bi, wanda basu da Wani zabin ma bayan hakan.




7. SIERRA LEONE;

Zaka iya daukar Luxurious bus ko private car wato motar gida, direct daga Lagos zuwa Freetown, Kuma zaka Isa can kafin hour 24, Freetown Shima sanannen garine da 'yan Nigeria ke zuwa a mota.




8. GUINEA;

Babban gari masu zaman Lafiya dake makwabtaka da Sierra Leone zaka iya tafiya a mota daga Nigeria kabi ta Cote D'Ivoire, ta Liberia ko sierra Leone. Zabi ya rage gareka ka zabi ta kasar da zakabi kaje can.




9. GUINEA BISSAU;

Idan ka zo daga Lagos ta hanya idan ka taho akwai karamin coastal county ana kiranshi Guinea Bissau, abin da ya kamata kayi ka tuka zuwa Conakry don ka samu mafi saukin connection da zai Kai ka Bissau. Ba wani abu Kuma da zai tsaida ka Kuma free kake kamar tsuntsu saboda kana cikin member na ECOWAS.



10. SENEGAL;

Garin da yake da manyan mutane a tsawo da kuma kyawawan 'yan Africa. A 1970s yawancin 'yan Nigeria suna tafiya Senegal ne ta mota. Akwai bus bus na zuwa Senegal direct. Duk lokacin da kaje Senegal da dole sai ka dawo da wani bread dinsu da yayi suna wannan shine babbar kyautar da zakai ma manya da Yara.

Comments