Main menu

Pages

KASASHE GUDA 2 DA BASU YADDA AYI SAKIN AURE

 



Kasashe biyu da Basu yadda da sakin Aure ba

Sun ce su fa abune mai matukar sauki ayi aure, amma sakin aure abune mai matukar wahala. Don haka a wasu kasashen ma suka mayar da dokar saki ya zama abinda bai kamata ayi ba.



Don haka su wadannan kasashen basu yadda da saki ba sam sam, su a nasu tsarin idan aka riga da akayi aure to shikenan fa sai dai mutuwa ta raba, kunga kenan ko da ace ana cutar da daya to dole yayi ta hakuri a wannan yanayin har ta Allah ta kasance.( Babu addini Mai dadi da kwatarwa kowa 'yanci irin Addinin Musulunci)




Kowace nahiya a Duniya ta yadda da sakin aure ga mazaunan cikinta amma akan wasu sharudda, amma banda Philippines da Vatican City. Wadannan kasashen biyu basu yadda da saki ba a kowane irin yanayi kuwa idan an daura to an daura kenan sai mutuwa.




Amma kuma su Vatican City sun yadda da zubar da ciki, ba wata doka da ta Hana su zubar da ciki (wa'iyazubillah) Amma kuma sakin aure Haram ne a wajen su. A Ghana saki da zubar da ciki dukkan su an yadda da ayi, ma'ana is legal. Amma a Vatican City da Philippines idan akai aure mutuwa ce kawai zata raba.




Dubunnan ma'aurata a sun gaji sun kasa hakura da wannan doka kullum suna nan suna jira suji cewa Philippines ta kawo dokar yadda da yin saki, saboda ma'auratan da suka gaji da zama da juna saboda cutuwa da daya keyi koma dukkansu, suna ganin ba zasu iya jurewa ba ace har sai mutuwa.


Shiyasa duk Wani tsari ko doka indai ba ta Musulunci bace to akwai qura.

Comments