Main menu

Pages

ABUBUWAN DA MUKE GUDA 6 DA YAKE LALATA MANA IDO

 .Abubuwa 6 Da muke yi Da Yake Illata mana Ido

Idanuwanmu sune fitilar jikinmu. Lokacin da Ido ke cikin duhu to kuwa tabbas gangar jikinmu na cikin hadari. Idanuwa sune manyan organ da ke taimaka ma jiki wajen kareshi daga cututtuka.Misali yanzu kazo zaka Sha Ruwa, idan ka duba ruwan kafin kasha, to zai taimaka wajen tsareka daga shan ruwan dake dauke da Kwan sauro ko Wani kwaron.To sai dai Kuma akwai abubuwa da mukeyi ko da sanin mu ko Kuma bamu sani ba da yake lalata mana idanu.1. Wasu daga cikinmu suna Kai idanunsu ga hasken rana. WebMD yace, hakan yana bata idanu, ya kamata ko zamu fiti cikin rana muna sanya sunglasses, a duk lokacin da zamu shiga ran.2. Wani lokacin kuma Muna Kai kanmu kusa da inda hasken wuta ke rattsatsi misalin wajen Yan walda karfe, to waxu na kallon wannan hasken dake tartsatsi. Don haka indai baka sanya face mask na walda ba to kar ka Kalli inda wutan take.3. Kar ya kasance kullum ana cikin hayaki, ko kuma wanda ya saba busa hayaki na wiwi ko taba, wannan hayakin na haifar da cuta a Ido kamar irinsu cataracts.4. Wasu Kuma suna shan giya ba tare da ka'ida ba kuma a hakan suke tunanin suna da lokaci mai kyau, to su sani a hankali hakan ke lalata masu wasu kwayoyin halitta na Ido, wanda hakan ka janyo matsalar gani.5. Wasu kuma suna kushe diga maganin ciwon Ido na eye drops, a lokacin da Ido ya canza kala zuwa ja, tabbas yawan amfani da eye drop na taba lafiyar Ido, ta hanyar hargitsa jinin dake tahowa zuwa Ido . Hakan kuwa zai kawo babbar matsala a gaba.6. Wasunmu kuwa sukan bata lokacinsu ne a kullum dare da rana suna gaban screen. Idan ba kallo muke a TV, to ana kallon Wani abin a waya ko system.


Yawaita kallon screen shima yana lalata Ido, ga masu yin aiki kullum a waya to su ringa kunna eyecare na wayar don rage hasken screen din.


Allah Ya sa mu dace Ya Kara mana Lafiya da zama Lafiya.

Comments