Main menu

Pages

MINAL IZZAR SO NA SHAN ZAGI AKAN ZARGIN KASHE MA GWANJA DA MAIMUNA AURE
Ana Zargin Minal Izzarso da kashe Auren gwanja


 Jarumar Minal Ahmad wacce aka fi sani da Nana Izzar so tana ci gaba da shan caccaka akan zargin kashe auren Ado Gwanja da Maimunatu, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.


Wannan ya biyo bayan hawa sabuwar wakarsa da ta yi mai suna Warrrr a ranar Juma’a tana kwasar rawa, hakan ya tunzura mabiyanta su ka hau caccakarta.
Jaruma Minal na shan caccaka kan zarginta da kashe auren Maimunatu da Ado Gwanja

Wannan ya samo asali ne daga wani bidiyo da Murja TikTok ta yi wanda ta yi shagube akan wata da ake zargin Minal ce, inda Munat Gwanja ta yi tsokaci tana zarginta da kashe mata aure.LH na wallafa a shafintaDaga nan ne mutane su ka gamsu da cewa akwai hannun Minal din a batun mutuwar auren Gwanjan.


Masu tsokacin sun hada da Nigerian wacce ta ce:

“Kin je kin yi snatchinga ai dole ki hau ki ce warrr.”


Mamansalim10 kuwa cewa ta yi:

“Kin kashe masu aure ai dole ki yi warr, ke dai ki ji tsoron Allah saboda kin raba mata da miji kema dai mace ce wallahi. Duniya ce ga ki ga ta.”


Adamu Adfar kuwa cewa ya yi:

“Tunda kin kashe mishi aure se ki aure shi ai.”


Queen kuwa cewa ta yi:

“Wa ya ce muku Minal ce raba su? Ku ji tsoron Allah.”


Kallamksaleh ya ce:

“Duk wanda ya yi wa Minal sharri shi da Allah. Kuma kar ki damu isa ki ka yi wallahi, sai ta Allah, makiya.”


Daga shafin Ado Gwanjan na Instagram ma koda ya wallafa bidiyon minal kamar yadda ya ke wallafa bidiyon daukacin ‘ya matan da su ka bi wakar tasa a dandin TikTok nan ma ya samu masu makamancin tsokacin da ake a shafin minal din.


Mixx_jiddah ta ce:

“Kin kashe mata aure kina bibiyarshi ko tom, Allah ya kyauta banza kaska kawai.”


aishamaiflour cewa ta yi:

“Uwar tsugudidi, bakin gulma da munafinci, shugabar majalisar kashe aure.”


Koma dai miye mu dai sai muce Allah Ya kyauta kawai. Idan zargine Kuma to Allah Ya saka mata

Comments