Main menu

Pages

YANDA ZA A GYARA BREAST YA CIKO

 
Gyaran Cikowar Kirji(nono boobs)

Babu kamar hulba yana gyara sosai kuma yasa kirjinki ya cicciko ya kara girma da kyau, wasu suna zuba garin hulba cikin abinci kullum suna ci don gyaran kirji in har abun ya zame masu jiki yana gyara sosai, kuma bayan cikar kirji ma yana warkar da cuttutuka da dama a jiki.
Haka kuma ana  iya samun kindirmo mai kyau sai ku hada da hulba asha Kuma yana aiki biyu ne farko gyaran kirji na biyu kuma sa ni'ima.

Ga wanda kirjin su ya kwan biyu suna iya hada garin sa da kundirmo, sannan su sami mansa suna shan spoon daya da safe daya da rana daya da marece, bayan haka ma suna iya dafa garinsa su tace su sa tsumma su gasa kirjin su da shi sannan kuma su shafa wa kirjin man.
Magana ta karshe anan kuma abin fahimta, ba'aso mace mai juna biyu ta sha hulba domin yana kawo nakuda da gaggawa. Na biyu mata masu shayarwa suna iya hada garin hulban a cikin abincin su yana kara nagartaccen ruwan nono, kuma zai sa jinjiri ya kasance cikin koshin lafiya.

Comments