Main menu

Pages

TURKASHI! WANI YA MAKA HADIZA GABON A KOTU SBD WA TAKI AURENSAI

Rigimar Hadiza Gabon da Wani Mutum

 A safiyar yau shafinmu hausaloaded yayi kicibis wanda abun kamar mafarki inda wani ya maka jarumar masana’antar kannywood kotu domin kuwa yace inda ba’a wasa da yaro to a bashi garinsa kamar yadda shafin Tonga Abdul Tonga


Wani mai suna Bala Musa ya shigar da karan fitanciyar ‘yar wasan Hausa Hadiza Aliyu da akafi saninta da suna Hadiza Gabon.Dan Shekaru 48 da haihuwa yace hakan ya zame masa dole ne ganin yadda Hadiza ta yaudareshi bayan data ci masa kudi kusan naira 396,000. Kudaden da yake bata a duk lokacinda ta tambayeshi kudi.
Bala yace babu abunda yafi bata masa rai irin yadda ya gayyaceta Gusau babban birnin jihar Zamfara taki zuwa bayan da ya kashe kudade domin zuwan nata.


Sai dai Gabon bata halarci zaman kotun ba a ranar Litinin din nan. Sai lauyanta Mubarak Bashir ya nemi kotun ta sake bashi dama a karo na biyu domin ya kawo wacce yake karewa. A ta bakin lauyan, ya sanarwa kotun cewa kanin Ita Hadiza ta shahara a duniya, hakan na iya zame mata hadarin idan zata halarci kotun ba tare da kyankyawan tsari ba.
Alkalin Malam Rilwanu Kyaudai dai ya daga karan zuwa 13 ga wannan watan da muke ciki inda ya baiwa lauyan damar ya kawo wacce ake karan.


Shi kuma Malam Bala, shi da yake neman aure menene kuma na gayyatar ta zuwa Gusau idan taje ta kwana a ina toh.


Kawai dai abun yayi kama da kila ya latsata ne bai samu tabi ba ya hasala ya shigar da kara da sunan zancen aure akan wasu ‘yan kudi kadan.

Allah Ya kyauta na gaba

Comments