Main menu

Pages

TURKASHI!!! WAKAR WARRRR TA ADO GWANJA TA TADA QURA...

 


Wakar WARRRR TA Tayar da Qura


Tofa! Jama'a ance wai ana wata ga wata. Kamar yadda kowa ya sani ne cewa Ado Gwanja ya shahara akan wakokin Hausa, inda tauraruwar shi take kan haskawa. Kuma wakokinsa kusan kaf dinsu Yana yi ma Mata ne inda yake yabon Matan da kurantasu da kambama masu, har ma ya nada ma kansa sarautar Limamin Mata.Saboda a cewarsa lokacin da ya fara Waka tun bai zama komai ba ba a ma sanshi ba, Matan ne suka karfafeshi, suka nuna Mai cewa Shima fa yana da basira da irin baiwar da Allah Ya yi masa. Suka ringa sauraren wakarsa a ko Ina kar ma gidan Biki, sannan idan Yana rerawa Matan ne dai suka damu dashi har suke tsayawa su kalleshi.To sai gashi yau kuma abin ya juya, inda shi Gwanjan ya fito da sabuwar Waka Mai taken WARRRR, yake zagi da aibata Matan nan da yake yabo a da, har yana dandankara zagi ga Matan duk a cikin wakar tasa, wanda mutane ke ganin wannan Waka musamman yayi ta don yaci zarafin Mata.  Duba da yadda Ake yo irin wadannan wakoki Kuma wasu Matan da Badu San darajar kansu ba suke rawar rashin kamun Kai da iskanci, ire iren wakar Ingallo. 
Idan har wakar Warrr da gaske anyi ne don cin zarafin Mata to kuwa hakan gaskiya bai kyauta ba Kuma bai kamata ba don su Mata daraja ce dasu matuka. Kar na cikaku da surutu ga wasu daga cikin martanin da wasu sukai akan wannan Waka ta Warrr tare da wasu baitoci na cikin wakar ita warrr din da wasu Matan suka hau.


Comments