Main menu

Pages

MAKUDAN KUDADE DA KADARORIN DA ATIKU ABUBAKAR YA MALLAKA TUN DAGA 1988 HAR ZUWA YAU.




 Kadarorin da Atiku ya tara a Duniyar nan


 -Atiku Abubakar ya mallaki hamshakin gida a birnin Washington DC mai tsawon taku 7,131 da dakuna 21 da guraren shakatawa wanda ya gina tun a shekarar 1988 akan kudin dalar amurka miliyan biyu da dubu dari tara da biyar ($2.95)


-Atiku Abubakar ya mallaki jirgin sama wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan biyu da dubu dari biyar ($2.500) wanda ya saya a shekarar 2015 domin yayi yawon takaran shugaban kasa.


-Atiku Abubakar ya gina jami'a mai suna AMERICAN UNIVERSITY OF NIGERIA ya kashe biliyoyin Naira kafin ya gina jami'ar, kudin da yake shiga masa a duk shekara ya kai ya ciyar da jama'ar garinsa.


-Atiku Abubakar ya mallaki wani katafaren kamfanni mai suna PRODECO LTD wanda ya kashe biliyoyin naira kafin ya gina kamfanin


-Atiku Abubakar ya mallaki wani kamfanin man fetur da sarrafa iskar gas mai suna INTELS NIGERIA LIMITED, ribar da yake samu a karkashin wannan kamfanin ya kai ya ciyar da al'ummar jiharsa gaba daya.


-Atiku Abubakar ya mallaki manyan jiragen ruwa masu dakon kaya daga kasashen turai zuwa Nigeria, irin manyan jiragen da sai sun shafe watanni 6 ana musu lodi sannan su shafe watanni shida ana sauke kayan da aka loda.


-Atiku Abubakar ya gina kamfanin ruwa mai suna FARO a jiharsa wanda ake sayarwa a dukkan sassan duniya, wanda a kullun ranar Allah yana samun ribar da yafi miliyon dari.


-Atiku Abubakar ya mallaki manyan kamfanoni a Nigeria da kasashen waje musamman daular larabawa Dubai, kashi 10 cikin 100 na masana'antun da ake dasu a Kasar Dubai Atiku Abubakar yana da hannun jari a ciki.


Jama'a Atiku Abubakar ya mallaki arzikin da bai kamata a samu talaka a jiharsa na Adamawa ba, amma hatta hanyar garinsa inda aka haifeshi ya kasa gyarawa duk da dunbin dukiyar da ya mallaka a duniya wanda shi kanshi bai san iyakarsa ba, ya kasa gyara hanyar garinsa har sai da shugaba Buhari yazo ya bada aikin kwangilar.


'Yan Nigeria kuyi hankali wajen zaben Atiku Abubakar, ba nufinsa ya gina Nigeria bane. Maganar gaskiya zaɓen 2023 cancanta zamuyi da Atiku yana son talaka da iyakar wannan tarin dukiyar daya tara da ya fara ma gyara hanyar garin sa da munga ƙananun attajirai ma suna yima umguwannin su tituna.


Don haka kafin mu zaɓe ka shugaban ƙasa 2023 sai ka nuna mana mai kayi don kar mu sake zaɓen tumun dare.


To Allah gamu a gare Ka wannan zabe na 2023 Ka zabo mana shugaba nagari wanda zai yi abinda ya dace ba son zuciya ba.

Comments