Main menu

Pages

KO KUNSAN KASA MAFI KANKANTA A DUNIYAR NAN?

 Kasa Mafi kankanta A Duniya

Duniya babban wajen, sannan akwai guraren abubuwan ban mamaki da in ka ziyarta zaka gani. Wasu daga cikinsu akwai mutane da yawa dake Kai ziyara duk shekara. Amma ba kowane wajene kowa ke iya zuwa ba, saboda wasu kasashen suna da tsauraran dokoki na wanda zasu shigo masu border.
Akwai kasashe da suke da abubuwan burgewa a kasashe daban daban a Duniyar nan da suke da al'adu ko dabi'u nasu na daban wanda zai zma abin burgewa. Don haka akwai wasu kasashe 'yar kanan da ko a cikin Map baza ka iya ganinsu ba.
Daya daga cikin wadannan kasashen itace Jamhuriyar Molossia, wadda take a Dayton, Nevada wadda take da mutane 33 kacal suke rayuwa a ciki. Wannan karamar kasa tana daya daga cikin kananan kasashen da muke dasu wanda suke da 0.2 square kilometers kacal na kasar yankin.
Wannan kasa Basu da jami'an soja ko police ko wani force. Sai dai Kuma suna daya daga cikin mafi kololuwar abubuwan more rayuwa a Duniya saboda tana da Matukar karfin tattalin arziki na GDP Capita.

Comments