Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI AKAN MAGUNGUNAN CUTAR CANCER
 Bayanai kan magungunan cutar kansa


Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake maganin ciwon daji shi ne halin wasu magunguna da ake kira chemotherapy, amma dumbin mutane musamman a wasu kasashen yammacin Afrika suna fargabar bin wannan hanya.Wasu daga cikin dalilin da ke sa mutane dari-dari da magungunan su ne illolin da ke tattare da su ta fannin kiwon lafiya.A Najeriya kasar da ta fi kowa yawan al'umma a nahiyar Afrika, wadannan magunguna na da tsadar gaske, bugu da kari kuma ba a ko'ina ake samunsu ba.Wani hadarin da masu cutar sankara ke fuskanta a kasar shi ne idan aka yi rashin dace wajen zuwa ga likitocin da basu da kwarewar bayar da magungunan.Cutar sankara ita ce cuta ta biyu da tafi kashe mutane a fadin duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya.WHO reshen Afrika ta ce, akalla mutane 8.8 miliyan ne suka mutu sakamakon ciwon daji a shekarar 2015.Sannan akalla kashi 70 cikin dari na wadannan mace-macen ana samunsu ne a kasashen da ke karanci da matsakaicin kudin shiga.Domin jin wasu halaye biyar da hukumar ta bayar da tace suna janyo wa masu yinsu ciwon daji, sai ku saurari shirin lafiya zinariya ta hanyar latsa makunnin da ke sama.

Comments