Main menu

Pages

AN DAURE WATA MATA SHEKARA 30 SBD LAIFIN ZUBAR DA CIKI

 


Matar da aka ɗaure shekara 30 a gidan yari saboda ta yi ɓari


An yanke ma wata Mata mai suna Karen hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari a El Salvador a 20215 bayan an zarge ta da zubar da cikiLokacin da Karen ta farka daga barci a wani asibitin El Salvador, ta lura cewa an saka mata ankwa a hannu sannan kuma ga 'yan sanda a gefenta."Akwai mutane da yawa a wurin kuma suna ta cewa wai na kashe jaririna kuma 'sai na fuskanci hukuncin abin da na aikata'," kamar yadda Karen ta shaida wa BBC.Tana buƙatar kulawar gaggawa saboda wahalar zubewar ciki. Amma Karen, mai shekara 22 a lokacin, ta tsinci kanta cikin zargin zubar da ciki."Na yi yunƙurin yin bayanin abin da ya faru, amma suka ƙi sauraro na," a cewarta.


An riga an yi min shari'a har ma an yanke min hukunci a can."


Tsattsaurar doka

El Salvador, da ke nahiyar Tsakiyar Amurka, na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke suka fi tsaurin doka kan zubar da ciki, wadda ta haramta duk wani nau'i na zubar da shi, ko da kuwa na barazana ga rayuwar mace ko an yi shi ta hanyar fyaɗe ko kuma 'yan uwa ne suka yi shi.Karen, wadda aka tuhuma da kisan kai, an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 30 a gida yari. Tana cikin rukunin mutanen da aka kira "Las 17", waɗanda aka taɓa yanke wa hukuncin ɗauri saboda yin ɓari ko kuma haihuwar jariri babu rai.Karen ta shafe shekara shida a garƙame kafin daga baya a sako ta tare da wasu mata uku a watan Disamban 2021 sakamakon wani matsin lamba daga ƙasashen duniya.


A lokacin da aka tsare ta, Karen na da ɗa mai shekara biyu.

Karen ba ta sake ganin sa ba har sai da ya kai shekara tara.

Comments