Main menu

Pages

AN CAFKE WANI SANATA DA ZARGIN CIRE SASSAN JIKIN MUTUM

 


An gurfanar da Sanatan Najeriya bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum


An gurfanar da wani dan majalisar dattawan Najeriya a gaban kotu bisa zargin kai wani yaro kasar Birtaniya da zummar cire sannan jikinsa.Ike Ekweremadu, mai shekara 60, da matarsa Beatrice Nwanneka Ekweremadu, mai shekara 55, sun gurfana a gaban kotun Majistiret ta yankin Uxbridge a Yammacin London ranar Alhamis.An mika wa gidan kula da kananan yara yaron, mai shekara 15, da ake zargi an kai London domin cire sassan jikinsa. Rundunar 'yan sandan birnin London ta ce hukumomi suna yin bakin kokarinsu domin kula da shi.Kotun ta saurari karar da ke cewa Mr Ekweremadu, wanda dan siyasa ne kuma lauya, ya taba zama mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Comments