Main menu

Pages

YANDA ZAKA HANA HACKERS, SUYI HACKING DINKA


 


 Hanyoyin da Zaka bi ka Hana ayi hacking dinka


 A yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.


Wannan wani Application ne Mai suna AVG Antivirus wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, kaima kar ka bari a barka a baya.
Mene amfanin wannan Application din?

Wannan Application din zai taimaka maka sosai gurin kare dukkanin sirrikunka na wayarka sannan zai hana hackers suyi maka hacking. Idan ka bashi dukkanin damar da yake bukata zai yi dogon binkice a wayarka daga baya sai ya nuna maka dukkanin abubuwan da zasu iya cutar dakai.
Sannan zai taimaka maka gurin kara saurin wayarka, kuma duk wani Application da yake aiki a background na wayarka wannan Application din zai tsayar dashi. Idan kana so ka dauko wannan application sai ka shiga play store, A nanne zaka ga komai na wannan Application din, na adadin mutanen da suka yi downloads dinsa da nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi, na tabbata da zakaji dadin wannan Application . Insha Allah

Comments