Main menu

Pages

ABUBUWA 6 DAKE BATTERY NA SAURIN TSOTSE CHAJI




Dalilai shida(6) dake sanya wayoyinku shan caji.


A yau zamu sanar daku abubuwan dake janyo yawan cinye cajin batirin waya musamman wayar android.



Wayoyin hannu a yau suna samun nagarta ne ta hanyar batiri me girma sosai, amma ingancin batiri shine abin lura ga mafi yawancin mutane masu amfani da wayar android. Hakan kuma shine yanayin fasahar wannan zamanin, hakan kuma ba yana nufin mu rinka saka waya a caji kowane lokaci ba. Idan har ka fahimci cewa cajin wayarka yana sauka da wuri ba kamar yadda yake da ba, ganowa abin dake haddasa wannan shine abin daya fi dacewa.



Wayar Android takanzo da tsarin batir iri daban-daban, amma batiri wadda ya kasance flat yama fi bada matsala sosai musamman lokacin da muke a wajen gida kuma muke cike da bukatar wayar mu, to saika ga a wannan lokacin kuma batirin ya shanye dukkan ragowar cajin dake dauke dashi.




A mafi yawancin lokuta zaka ga kana caja wayarka tayi awa daya ko fiye da awa tana caji amma kuma abin haushi sai cajin ya kare a kasa da sa’a daya. Abinda ya kamata ka sani shine akwai abubuwa da dama a  kasa wanda baka sansu ba/ka sansu amma baka san illarsu ga rayuwar batirin wayarka ba, kula dasu kuma da daukan matakin daya dace akansu zai karawa batirin wayarka karfi da dadewa batare da wata mishkila ba. So,yanzu ga wadansu daga cikin abubuwan da suke janyo cinye cajin batiri.



1. Brightness

 Zamu fara daga abinda yake sananne wajen cinye cajin batir ko kuma kashe batiri ma gaba daya shine: Screen Brightness.


Kamar yafi dadin sha’ani idan kakai hasken screen din wayarka karshe, musamman idan kana wurin da yake me haske, amma kuma yin hakan yanada matukar illa ga batirin wayarka. Abu na gaba, kurewa brightness kuma kana amfani da light mode wannan kan iya kashe batiri cikin gaggawa. So, abinda yafi dacewa shine rage hasken screen domin saving din caji da lafiyar batiri.



Amma kuma a wani bangaren, ragewa brightness yayi duhu sosai bashi da dadi, musamman idan kana da matsalar ido ko kuma kana wurin haske me karfi sosai. Abinda ya kamata kayi shine a maimakon ka rage brightness dinka yayi duhu har ta yadda bazaka iya gani ba, zabi mafi kyau shine kashe wayarka sannan apps din daka fiye amfani dasu yau da kullum (kamar Instagram da facebook messenger) saika saka su a dark mode.




Wannan bawai zai saka screen din wayarka yayi duhu yadda zai dameka ba amma zai canza asalin farin screen din wayarka da kuma background na app din wayarka zuwa baki dai dai da bukatar ganinka. Zakayi mamakin yadda zai taimaka wajen ajiye extra caji na bitirin wayarka dama lafiyar batiri kuma ya dauki lokaci mai tsawo batare da wata matsala ba.




2. Apps na background

Su kuma background apps galibi suna aiki ne koda baka amfani dasu kai-tsaye. Misalin wadannan apps sun hada da VPN, anti-virus, da kalanda apps. Su wadannan apps suna kula da wasu abubuwa na wayarka batare da kai ka shiga tsakaninsu ba, wadda kuma yawan aikinsu akai-akai kan jawo shan caji. Abu na gaba shine baka da bukatar kasan adadin wadannan ire-iren apps da suke aiki a kasa ba tareda saninka ba, to ya za’ayi kenan?.



Idan kana amfani da wayar android ka tafi zuwa Settings sannan ka danna “Device Care” ko kuma “Batiri” ga masu amfani da iPhone. Zaka ga wurin dai dai ta batiri wato batiri optimazation, wadda idan ka kunna shi wato activation zai rufe duk wasu background apps da suke aiki ba tareda izininka ba. Kuma wannan zai karawa batirin wayarka lafiya da inganci, so yanada kyau a lura da wannan kwarai da gaske.




3. Hada hoto da hoto Mode

Idan kana yawan amfani da YouTube premium ko Twitch ko ire-iren wadannan apps akan wayarka, zaka rinka ganin ko amfani da wadannan fasahohin na hoto cikin hoto mode. Shi wannan tsarin shine kallon ko wane irin bidiyo a cikin wani karamin akwatin kallo acikin screey din wayarka kuma a dai-dai wannan lokacin kana amfani da wani app din daban, wanda yin hakan yana da dadi amma ka sani yawan yinsa kuma da’iman kan sa batiri ya mutu da wuri.




Zaka iya dakatar da fasahar hoto da hoto mode idan ka tafi zuwa matakin saiti na gaba saika zabi app din da kake son dakatarwa saika yi disabling nashi.




4. Zama ko yaushe kana amfani da waya ba tare da hutu ba 24/7

Yawan yin amfani da waya ba dare ba rana kullum yakan jawo mutuwar batiri, kuma ma ba abin birgewa bane mutum ya kasance kowane lokaci yana amfani da waya dare da rana saboda a dukkan lokutan kana karbar notificationn, background updatet da wasu sakonnin da kai kanka ma baka da bukatarsu.




Lokacin baccin ka lokaci ne daya kasance me girma a gareka daya kamata ka kashe Wi-Fi. Tabbas zaka iya kashe ko saka wayarka a Airplane Mode. Amma idan baka son a kiraka ba’a sameka ba ko kiran gaggawa to saika kashe iya Wi-Fi da data yadda idan an kiraka za’a sameka. Zaka iya haka  a wayarka idan ka tafi zuwa Wi-Fi and Mobile Data settings saika kashe su duka deactivate kenan. Amma ka lura da cewa saka waya a “Do Not Disturb” mode baya dakatar da ko kashe Wi-Fi ko data.




5. Amfani da tsohon batiri

A wani lokacin kuma, ba laifin app ko kuma rashin saitin waya ke taba lafiyar batiri ba amma kuma wani lokacin matsalar batirin ne da kansa. Kamar yadda komai yake, itama waya takan zama tsohuwa wata rana, sannan yau da gobe ba zaisa batirin wayarka ya zama kamar yadda yake a farko ba. Bayan shekara biyu ko uku (wannan ya danganta da model din wayarka), batirin wayarka bazai zama karfinsa irin na farko bane, wanda hakan ke kaiwa zuwa saukar caji da sauri. So, meya kamata ayi dangane da wannan?




Abu na farko mafi dacewa tukuna shine canza batirin gaba-daya. Hakan shi yafi sauki daka sake wayar gaba daya kuma yin hakan zai gyara matsalar batirin wayarka cikin sauki ba tareda wata matsala ba. Farashin batir yana bam-bamta amma ya danganta da irin wayar da kake amfani da ita. Misali batirin Samsung Galaxy S9 yakai naira dubu hudu, na iPhone 11 kuwa a wani bangaren zai ninka hakan. Toh koma dai yaya ne sake batiri bazai jigata asusun bankin ka ba yayin sakewa.



Zabi dai mafi tabbas shine sake batir baki dayansa. Amma kuma zaka iya samun kanka a wani matakin da za’a ce maka a cire ko replacement na edge, a wannan matakin kawai sake batir shine mafi a’ala.




6. Apps masu aiki da Track Location

Akwai apps masu dunbin yawa da suke tracking din inda kake. Google Maps, Bumble, Deliveroo, Retail Apps da wasu da yawa. Wani zaiyi tunanin cewa wadannan apps suna tirakin inda kake ne kawai yayin amfani dasu kai tsaye, amma wannan bashine damuwar ba. Suma suna cinye caji idan ka barsu a kunne ko yaushe. Tayaya za’a kaucewa wannan kuma?.




Hanya mafi sauki wajen dakatar da ire-iren wadannan apps shine kashewa phone’s location gaba daya. Zaka iya haka a cikin wayarka idan ka janyo labulen sama ko kuma kai tsaye ka nufi Settings ka shiga “Location options” saika kashe su baki daya. Idan kuma kana son wasu daga cikin apps(wataqila ko kanason safety ko navigation app) suci gaba da tracking na location dinka, zaka iya dakatar dasu daya bayan daya ta hanyar “permission” saika saita ko wanne app,yin haka zai dan dauki lokaci amma hakan kuma dai zai baka damar sanin adadin apps din daka yarda suyi tracking na location dinka a lokacin daka so.




Wannan sune a takaice hanyoyi shida daza kabi ka rage cin cajin wayarka da inganta lafiyar batirin wayarka.

Comments