Main menu

Pages

MATASAN JIHAR SOSKOTO SUN FUSATA SUN FIYO ZANGA - ZANGA

 



Zanga-zanga ta ɓarke a garin Sokoto na arewacin Najeriya, inda matasa ke ci gaba da nuna ɓacin ransu kan kalaman ɓatanci da ya jawo kisan wata matashiyar ɗaliba mai suna Deborah Samuel.


Masu zanga-zangar na neman jami'an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).


Matasan maza da mata suna aiwtar da zanga-zangar a wurare daban-daban a fadin Sokoto tare da ƙona tayoyi, da suka haɗa da Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III. Kazalika wasu sun yi cincirundo a ƙofar gidan gwamnatin jihar.


Rahotannin da BBC ta samu sun nuna cewa da farko zanga-zangar ta lumana ce, daga bisani sai ta rikide ta zuwa tamkar rikici, inda mutane suka dinga jefa duwatsu kan gidan sarkin Musulmin.


Wani da BBC ta zanta da shi da ke kusa da fadar sarkin a lokacin da abin ya faru ya ce jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da matasan kutsawa fadar.

Comments