Main menu

Pages

KO KUNSAN ILLAR DA NA'URORIN ZAMANI KE HAIFARWA KANANAN YARA?




Ci gaban fasahar zamani da ake samu na taimakawa wajen bunkasar al’umma, sai dai hakan ta wani bangare na janyo hadari ga lafiyar kwakwalwa da jikin yara kanana.


Hakan na faruwa ne a sanadiyyar kwashe tsawon lokaci da wasu yaran ke yi suna wasanni a kwamfuta ko a wayar komai da ruwanka da talbijin da ma sauran na'urorin zamani. In ji likita.


Wasu daga cikin illolin da amfani da wadannan na'urori fiye da kima ke yi wa yara sun hada da, dakushewar basira da janyo musu teba, lamarin da ke sanya zuciya ta yi rauni.


Haka kuma yawan amfani da na'urorin kan rage wa yara karfin ido, ya janyo musu ciwon kai, sannan ga lalata zamantakewarsu da sauran yara.


Yawan kallo da wasanni da na'urorin fasahar zamani idan ya yi tsanani ya kan janyo rayuwarsu da tunaninsu ya takaita ga abubuwan da suke gani a cikin na'urorin. A cewar kwararrun likitocin yara.


Wani kamfanin mai zaman kansa da ke harkokin tsaro a Burtaniya mai suna Norton, ya yi wani bincike inda ya gano cewa iyaye na damuwa kan yadda yaransu ke yin amfani da wayar hannu fiye da kima.


Hakan na kunshe ne a wani rahoto da shafin intanet na BBC ta fannin fasaha ya wallafa a watan Nuwambar shekarar 2018.


Binciken ya kuma nuna cewa kashi 43 cikin dari daga cikin iyaye 7000 da aka yi binciken a kansu a fadin nahiyar Turai, sun nuna damuwa kan yadda yawan amfani da na’urorin fasahar zamanin ke hana ‘ya’yansu samun isasshen barci.


An dai yi binciken ne a kan yara ‚yan shekara biyar zuwa masu shekara 16 inda aka duba tsawon lokacin da suke kwashewa a kan na’urorin da abubuwan da suke yi da su.


Sakamakon bincike ya nuna cewa yara a yanzu sun fi kwadayin su yi amfani da wayoyi da kwafutocin tafi da gidanka fiye da yadda suke kwadayin alawa da kayan zaki.

Comments