Main menu

Pages

KASUWAR CRYPTO TA FADO KASA WARWAS
 Kasuwar kudin intanet ta Crypto ta fadi kasa warwas, bayan darajar kudin mai matukar farin jini ta rikito da kashi 99 cikin 100, inda hakan ya yi awon gaba da wasu kudaden irin shi.


Darajar kudin intanet ta Terra Luna ta fadi daga kololuwar darajar dala 118, kwatankwacin naira 70,210 a watan da ya gabata, zuwa dala 0.09 a ranar Alhamis.


Wannan faduwa ta shafi darajar kudin intanet na TerraUSD, wanda a baya yake da darajar ba yabo ba fallasa.


Yawancin masu hannun jari da ke amfani da kudin sun fara janyewa daga manyan kamfanonin crypto, lamarin da ya sanya kasuwar tangal-tangal.


Sai dai kamfanonin da ke sa ido wajen ganin an samu daidaito a wannan fannin, na kokarin ganin ceto fannin daga durkushewa baki daya, misali inda suke sanya darajar ko wanne sulen crypto kan dala 1 maimakon 0.09.


A ranar Alhamis darajar kudin TerraUSD ta fadi zuwa dala 0.04, kamar yadda shafin intanet mai tallan kudin intanet na Coin Market Cap ya bayyana.


Ita ma darajar fitaccen kudin intanet na Tether, ta fadi zuwa kasa da dala 0.95, lamarin da ba a taba gani ba.


Kalmar "cryptocrash" ce mafi shahara da wadari a shafin Twitter da kuma binciken Google. A kasuwar bai daya darajar kudin crypto ta kai dala Tiriliyan 1.12, kusan kashi uku ta darajarsa a watan Nuwamba, inda ya kai kashi 35 cikin 100 na hasarar da ya tafka a cikin makon nan.


A yanzu duk sule daya na Bitcoin ya kai darajar dala 27,000, kamar yadda Coin Market Cap ya bayyana, wannan ita ce mafi kankantar daraja tun watan Disambar 2020, da kuma rikitowa daga kololuwar darajar dala 70,000 a shekarar da ta gabata.


Shi ma kudin intanet na biyu mafi daraja wato Ethereum, ya samu koma baya da kashi 20 cikin 100 cikin kasa da awa 24.


"Wato faduwar darajarar TerraUSD ta fara ne bayan firgici da tsoron da masu zuba jari suka fara nunawa, lokacin da aka fara rade-radin su gaggauta kwashe kudin tun kafin goguwar karyewar darajar kudaden crypto ta shafe su," in ji Bafaranshen nan masanin tattalin arzikin kudin intanet wato Coppola.


"Faduwar gaba da firgici ne ke bada lamura a nan."


A ranar Juma'a kamfanin Terraform da ya kirkiri kudin intanet na TerraUSD da Terra Luna, ya yi nazari kan halin rashin tabbas da ce-ce-ku-cen da ake yi kan dakatar da hada-hadar kudaden.


Nan da nan kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter, tare da bayanin an dauki matakin ne domin samun damar nazari da shawarar ''yadda za a farfado da darajarsu.''


Tun da fari, wanda ya kirkiri Terraform Labs, Do Kwon, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ina sane da cewa kwanaki uku da suka gabata masu tsauri da damuwa ne a gare ku.


"A yanzu da na dukufa ganin an samu hanyar warware wannan matsalar, ina fatan za ku bada hadin kai domin sake gina darajar kudinmu."


A bangare guda kuma, wani sashen kamfanin da ya ware inda masu zuba jari ke samun damar tattaunawa kan batutuwa irin wannan, ya wallafa wata sanarwa da ke cewa ''sun dakatar da shi.


Hakan na nufin sabbin abokan hulda ko masu zuba jari ba za su shiga ba, hakan ya ɗarsa tsoro da rashin tabbas da rashin madafa kana da yada bayanai masu daga hankali".


A Tether kuwa, shugaban da ke kula da bangaren fasahar intanet ne ya wallafa bayanin karfafa gwiwa ga abokan huldarsu a shafinsa na Twitter, tare da jaddada kamfanin na da isassun ruwan kudi a asusun kar-ta-kwana, domin biyan duk wanda yake da ra'ayin saida hannun jarinsa.


Paolo Ardoino ya wallafa a Twitter: "[A] tunatarwa cewa Tether na mutunta abokan hulda [Tether] na da kudi daga dala miliyan 1 zuwa miliyan 300, idan kuna son a maido kudin ku ba tare da bata lokaci ko fuskantar asara ba."


Tsauraran dokoki

Jami'ai da 'yan majalisu a wasu kasashe sun yi kiran a tabbatar an fito da wani tsari mai inganci kan kudaden crypto.


Sakatariyar baitil malin Amurka Janet Yellen ta ce ya kamata a dauki matakan kauce wa faduwar darajar TerraUSD, ta yi kalaman ne a zaman majalisar dokoki ranar Talata.


"Cikin sauki ta bayyana wanna kudade ne masu daraja, to amma a bayyane take akwai hadari da fargabar rashin sanin inda aka dosa idan ana batun samun daidaito da tabbacin samar da hanayr dorewar darajarsu, abu ne mai matukar muhimmanci ayi hakan," in ji ta.


Wani rahoton baitil malin Amurka na watan da ya gabata, ya bayyana shirin fito da tsarin da zai taimaka wajen dorewar darajar kudin intanet, wanda akai amanna da cewa nan gaba kadan "zai kasance hanyar biyan kusan duk kayan da aka saya musamman ta intanet".

Comments