Main menu

Pages

     


     Kayan Hadin Sinasir


Kayan hadi:-

-Farar shinkafa ta tuwo

-Backing powder

-Suger

-Yeast

-gishiri

Yadda zaki hada


Dafarko uwargida zaki wanke shinkafarki saiki dafa wata daban ki hada akan danyar ki bayar a markado miki, saiki sa yeast da suger da backing powder, zaki iyasa gishiri kadan saiki juya kamar dai yadda ake kwabin wainar shinkafa amma kwabin sinasir yafi na wainar shinkafa ruwa, saikiSa arana in ya tashi saiki dauko kaskon suya kisoya mangyada da albasa saboda wani man yanada wari in kika soya saiki juye akwano, saiki sami auduga maikyau ko brush din girki, saiki dinga dangwalo man dashi kina shafawa a kaskon saiki zuba kullin kirufe kibarshi zuwa yan mintuna saiki cire ba ajuya sinasir haka zakiyi tayi harki gama,sai ayi miya maikyau aci da ita.

Comments