Main menu

Pages
BURGER


Ingrediants :

Flour
Yeast
Gishiri
Kwai
Butter
Dankalin turawa
Salak
Ketchup
Salad cream
Nama
Albasa
Maggi
Spices
Tumatur
 

YADDA AKE HADAWA

 

Da farko zaki samu flour daidai bukatarki sai ki tankade acikin bowel, sai kisa gishiri kadan da yeast ki kwaba da ruwan zafi, amma bamai zafi sosai ba.


Kwabin yayi kamar na bread, idan kin gama kwabawa sai ki saka shi a rana ki barshi yayi 20min, sai ki sami gwangwanin gashi ki shafa butter ajiki sai kisa kwabin flour aciki.Sai ki gasashi a oven, idan ya gasu zakiga bayan yayi brown sai ki ciroshi ki rabashi 2.

Already kin wanke nama kin tafasa tare da maggi da albasa, amma naman zaki dakashi kamar na dambu sai ki soyashi sama~sama.Sannan ki wanke dankali ki yankashi kamar cube sai ki dafashi, kwai dinma dafashi zakiyi, sai ki yankashi atsatstsaye.Sannan ki dauko wannan bread din da kika raba 2 sai ki shafeshi da salad cream gaba da bayansa, sannan ki dada shafa masa ketchup, sai ki dauko salad wanda kika wanke kisa akan bari 1 na bread din, amma fa ba'a yanka salad din.Sai ki dauko soyayyen namanki kisa akan salad din, tare da yankakken dankalinki da kwai, sai kisa yankakken tumatur da albasa already kin wanke kinyi masa yankan circle.

Bayan kingama saka dukka abubuwan sai ki dauko dayan bread din kirufeshi, idan kinaso zaki bayan kingama hadin sai ki kara gasashi sama~sama ko kuma aci haka.


Comments