Main menu

Pages

HUKUNCIN SHEKARA 15 GA DUK WANDA AKA DAUKAR MAI DAN UWA YA KAI KUDIN FANS A...!!!.

 Majalisar Dattijan Najeriya ta zartar da wani ƙuduri da zai tabbatar da hukuncin ɗaurin aƙalla shekara goma sha biyar ga masu biyan kuɗin fansa don kuɓutar da wani da aka sace.

Ƙudurin dokar ya kuma amince da hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane.

Ƙudurin, wanda gyaran fuska ne ga dokar yaƙi da ta'addanci, ya ƙunshi ɗaurin rai-da-rai ga masu satar mutanen da kotu ta kama da laifi, kuma matukar satar ta kai ga mutuwar mutum, masu laifin za su fuskanci hukuncin kisa.

Bangaren da ke cike da ka-ce-na-ce a ƙudurin dokar dai shi ne wanda ya nemi ɗaure duk wani mutumin da ya biya kuɗin fansa ga masu satar mutane.


Hukumomi sun yi amanna cewa biyan kuɗin fansar na rura wutar sace mutane a Najeriya, kamar yadda suma 'yan majalisar dattawan suka yi imani da hakan.


'Yan majalisar Dattijan, sun ce idan aka zartar da kudirin, zai tsame Najeriya daga cikin kasashen da ake rura wutar aikata laifuka wajen biyan kudi.


Wasu masu lura da al'amura a kasar sun ce mayar da batun laifi, zai sanya iyalan mutanen da aka sace waɗanda idonsu ya rufe kuma ba su da yadda za su yi ciki mawuyacin hali saboda ƙarancin matakai daga mahukunta na kare aukuwar sace mutane tun da farko da hanzarin ceto mutanen da aka sace idan abin ya faru.


Za a tafka muhawara kan ƙudurin dokar a majalisar wakilai kafin aikawa shugaban ƙasar don ya sa hannu, lamarin da zai iya kwashe makwanni ko watanni.


Nijeriya dai na faɗi-tashi wajen shawo kan miyagun sace-sacen mutane da gungun 'yan fashin daji waɗanda suka sace dubban mutane a cikin shekarar da ta wuce.


Fiye da shekara 10 ke nan wasu gungun bata gari da ake kira da 'yan fashin daji ke tayar da zaune tsaye musamman wajen kai hare hare kauyuka da garuruwa da kuma satar mutane don neman kudin fansa.


Yawanci dai su kan sace dalibai ko mazauna kauyuka da kuma wadanda ke tafiya a kan manyan hanyoyin musamman a jihohin arewacin kasar.


Karin bayani

A kwanakin baya, majalisar wakilan Najeriyar ta buƙaci a soma toshe layukan wayoyin mutanen da aka yi garkuwa da su.


Majalisar ta ce ta hanyar toshe layukan waɗanda aka sacen, 'yan fashin daji za su rasa hanyar cinikin kuɗin-fansa da dangin mutumin da suka sace.


Masana harkar tsaro na cewa da zarar an samu hadin-kai tsakanin jami`an tsaro da hukumomin da ke yaki da masu aikata laifukan da suka shafi kudi, da kuma cibiyoyin da ke hada-hadar kudi, da wuya miyagu su sha idan sun yi damfara ko sun karbi kudin fansa ta banki.

Comments