Main menu

Pages

KO KINSAN ILLAR SAKA MATSATTSEN PANT KO WANDO?

 Saka Matsatstsen Wando Na Yi Wa Gaban Mata Illar Gaske –In Ji Binciken Ƙwararru  


A sakamakon wani bincike da wani ƙwararren likitan mata, mai suna Tony Mbume ya yi ya nuna cewa akwai matuƙar illa da tashin hankali ga matan da ke saka matsatstsen wando.


Kamar yadda Tony ya bayyana, tashin hankalin shine yadda shi gaban mata ke zama a toshe matuka, iska baya shiga saboda matsatstsen wando da suke saka wa. Hakan na haifar da wasu cututtuka dake illata gaban nasu.” Maimakon a rika saka irin wadannan wanduna dake hana gaban mata samun isasshen iska sannan ya kawo illa matuka, kamata yayi a rika saka wanduna wanda ba a yi su da laida-laida ba ana nufin irin wanda aka yi da yadi-yadi, wato auduga.Tony ya kara da cewa babbar matsalar da ake samu shine shi gaban mata idan baya samun iska akai-akai toh ya kan dau zafin gaske da hakan ke haifar da matsaloli masu dama ga mace.Ya kara da cewa baya ga nan, hakan kan haifar da sai mace ta ga gaban ta na saba da kuma wasu kuraje na fitowa duk domin irin matseshi da ake yi.A karshe ya yi kira ga mata da kuma roko hannu bibbiyu da su rika saka wanduna masu alawus sannan idan dare yayi a rika dan barin gaban yana shan iska a lokacin da za a kwanta barci.


” Hakan na sa gaban ya tsantsane, ya bushe kuma a samu lafiya kafin safe.” Inji Likita Tony.

Manufar Mu A Kullum Itace Domin Wayar da Kan Al'umma,_

_Domin magance matsalolin 'yan mata da kuma matan aure har zaurawa.

Comments