Main menu

Pages

KARIN BAYANI AKAN ZARGIN KASHE AHMAD S NUHU

 Rashida Mai Sa'a, Ta yi qarin bayani.


Kwanakin baya ne aka ci karo da wani video da tsohuwar Jaruma Safiya Musa tayi a live dinta na TikTok. Inda maganar taso tada kura, wanda tun lokacin da take wannan video ake ta kiranta ana cewa ta dakatar da wannan maganar da take yi. 


Amma hakan kamar ana qara ingizata ne, don kuwa sai da ta kai aya sannan. To shi dai Ahmad S Nuhu a qalla yanzu ya Kai Shekara 15 da rasuwa, Kuma ko ma dai menene kwanan shine suka kare, sannan Banga amfanin rashin tashinar ba, addu'a da fatan samun Rahaman Allah shine abinda yafi buqata yanzu tunda dai ya riga da ya bar Duniyar Kuma har gaba da abada ba zai taba dawowa ba sai dai mu muje can mu taras da wadanda suka tigamu.


To Amma fa idan aka duba ta wata fuskar zaku gane cewa shi jinin Dan Adam baya taba zuba a banza duk munafincin da za ayi da rufa rufa komai tsawon lokaci to fa wannan mugun abun da akai sai ya fito ya bayyana a Duniya. Kar ma ace matsala irin Wannan ta kashe rai. Duk da cewa dai zancen zargine ake har yanzu.

Ba tare da na cika ku da surutu ba ga video Rashida Mai Sa'a da tayi bayanin yadda abin ya kasance don kuwa tare suka tafi da Ahmad har suka isa sokoto, inda tace ita ana tace ya barta shi Kuma zai wuce Maiduguri. Ku Kalli video don Jin ta bakinta
Comments