Main menu

Pages

INA MAI SON KATON BENE A ALJANNAH?

 



INA MAI SON KATAFERAN BENE A ALJANNA??


Hakika dukkan wanda yake son Mallakar wani gida a nan duniya to babu makawa sai ya dage wajan neman kudi da kayan aikin gidan gidan ko abinda zaiyi amafani da shi na saye wannan gida,dan Haka wani kokari da tanadi kake dan samun babban bene a aljanna??.


Lallai Manzon Tsira Farin jakada Annabi s.a.w ya baiyana al'ummarsa dukkan wani alkhairi da zai kaimu samun aljanna cikin sauki, kuma yayi mana gargadi da dukkan abinda zai kaimu shiga gidan wuta.


Lallai benan Aljanna baya samuwa sai ga wanda yayi kokari wajan aikata kyakkyawan aiki da kyakkyawan Niyya da biyayya ga Annnabi s.a.w

Da sauran aiyuka wanda dukiya ko 'ya'ya basu bakasu agobe alqiyama sai wanda yajewa Allah da zuciya kubutacciya


DAGA CIKIN HANYOYIN SAMU BENE A ALJANNA


Daga Abi Malik Al'ash'ary R.A yace: Annabi s.a.w yana cewa:

(Lallai acikin aljanna akwai wani bene,wanda ana ganin cikinsa daga wajensa,kuma ana ganin wajensa daga cikinsa, Allah ya tanadi wannan benene ga wanda:

-Yake Sassauta magana

-Kuma yake ciyar da abinci

-Kuma mai yin azumin nafila

-Mai yin Sallah alokacin da mutane suke barci)

#صححه الألباني.


Daga Abdillah bn Amru R.A yace:Manzon Allah s.a.w yace:

( (Lallai acikin aljanna akwai wani bene,wanda ana ganin cikinsa daga wajensa,kuma ana ganin wajensa daga cikinsa) sai Abi Malik Al'ash'ary R.A yace:Na wanane ya Manzon Allah sai yace:

(Na wanda yake dadadi magana ga mutane,kuma yake ciyar da abinci kuma ya kwana yana ibada alokacin da mutane suke barci).

@صححه الألباني.


Allah ka sanya mu aljanna firdausi.

Comments