Main menu

Pages

FACE SETTINGS (MAKE UP TUTORIAL)

 Yadda Ake Setting Na Fuska

Bayani akan yadda zakiyi setting fuskarki gaba daya da setting powder, sannan ki setting contour dinki da highlights dinki da nasu setting/ finishing powder din.Yadda zakiyi setting fuskarki gaba daya adena ganin wani danshi ko maiqo daya hada da na foundation, highlighter da kuma contour.


Zaki samu powder dinki mai gari wadda ta dace dakalar foundation dinki da kika shafa, da brush/sosonki na shafa powder, saiki dangwali wannan bushasshiyar powder din da muke kiranta setting powder kidan karkadeta barbadanta yadan ragu yadda ba zatai miki dabbara dabbaraba, kidinga daddannawa ahankali ahankali kina bi lungu da saqo na fuskarki kina haka harki gama, sai kinga komai yayi smooth (sumul sumul) ba sauran danshi ko maiqo na foundation ko kuma highlighter ko bronzer saiki barshi. Abunagaba daxakiyi shine ki setting din wuraren dakikayi highlight da contour da setting powder dinsu , Wanda shizaisa kwalliyar taqara armashi.( ba aso kiyi setting din fuskarki gabadaya da powder wadda tafi foundation din dakikashafa duhu)Yadda zakiyi setting highlight dinki shine, kidakko busashyr highlighter kokuma kisamu Ben nye banana powder kokuma baby powder musamman Johnson ( acikin ukunnan zaki iya yi da kowanne) dinki kishashafa awuraren dakikai highlight da cream highlighter. Haka shima contour din kisamu busashshyar bronzer dinki ki setting inda kika shafa bronzer kokikai contouring saikiga sunyi daidai sunyi das.Wannan shine yadda ake setting highlights da contour dakuma fuska gabadaya.Saikuma shafa blush inkinaso, amma shafashi yanaqarawa kwalliya kyau. Yadda xaki shafa blush shine zakishafashine akan kumatunki ki blending dinsa sosai. Kuma anaso inzaki shafa blush kidanyi murmushi sannan kishafa. Inkikai haka zaifi baki result din kwlliya mekyau.Abubuwan daxaki yi contour dasu sunhadada:


contour kit (daya hadada cream da powder)

foundation din datafi wadda kikashafa duhu.da powder din datafi wadda kikashafa duhu

jambaki dark brown ba me qyalliba

brown brow pencil( brown din jagira).

Gel liner brown. Dadai sauransu


Wadannan sune abubuwan da ake iya contouring dasu. Kubiyoni domin jin yadda zaki shafa jambaki, lipstick/ lip glows dakuma yadda zakiyi concealing din baki yabada shape mai kyau.

Comments