Main menu

Pages    DABARUN GIRKI

** Idan stew naki ya kone toh ki samo wani tukunyan sai ki kwashe sama saman stew din kisa a wani tukunyan sai kidan sa sugar yin hakan zai hanajin teste na konewa.


** Idan zakiyi an fani da tafarnuwa (garlic) a miya toh ki fara soya shi tare da albasa yin hakan zai hana shi wari a baki ko ya fita a nunfashi.kuma anfani da tafarnuwa a abinci yana da kyau sosai.


** Idan zakiyi anfani da su green beans kuma bakya son colour din ya changer toh sai kiyi boiling nasu da baking powder.


** Idan zaki dafa ganda ko kayan ciki kuma bakida pressure pot toh ki sa cokali aciki zaiyi saurin nuna.ko ki wanke da ruwan khal


** Duk sanda zakiyi marinating na nama ko kifi kina sa lemun tsami aciki akwai sirri.


** Idan zakiyi stew ki fara taffasa kayan miyan kafin kiyi blending.


** Uwargida idan kina son kifinki yayi dadi toh ana gobe zakiyi anfani dashi ki soya ke kanki sai kinfi jin dadin ci.


** Idan kina son ki gane kwai mai kyau sai ki zuba su acikin ruwa zakiga masu kyau din suna kasan ruwan mara kyau kuma zasu tashi a saman ruwan.


** Yanada kyau idan zakiyi masa bayan kinyi hadin sai kisa hannunki aciki ki juya shi hakan nasa shi yayi tashi mai kyau.


** Idan gishiri ya yawa miki a miya ki fere dankali kisa aciki.


** Idan zaki yanka red pepper dinki ki shafa hannunki da man gyada yin hakan zai hanake jin zafin shi.


** Idan zaki yanka albasa kuma kina tsoron zafinshi a ido to bayan kin bare bayan kisa a fridge zuwa minti biyar ko kina yanka albasan acikin ruwa hakan zai hana zafi a ido.


** Amfani da cray fish a abinci yana da balain kyau


** Idan zakiyi ajiyan madara bayan kinyi anfani dashi kuma kina gudun kar ya bace ko ya changer teste to kidan sa gishiri aciki.

Yanada kyau kina anfani da curry leave da scent leave a abinci musamman a pepper soup.

Comments