Main menu

Pages

MAKE UP TUTORIAL (SHAPES DIN FUSKA)

 SHAPES NA FUSKA

A darasin mu na farko da mukai akan kwalliya, munyi bayanin gaba dayan kayan kwalliyar da yadda ake amfani da kowannensu.


Darasisin mu na yau shine kisan wane irin shape din fuska gareki kafin ki fara kwalliya.

Sanin shape din fuskarki shi zai taimaka miki wajan tsara kwalliyar data dace da irin wannan fuskar. Kowane mutum akwai shape din fuskarsa, Wanda idan masu shapes din fuska daban daban sukace zasu kwaikwayi irin kwalliyar me wani kalar shape din, to a zahirin gaskiya kwalliyar bazata zauna tayi yadda ake soba.


         Shape din fuska sun hada da:

              1=oval shape

              2=long shape

              3=Round shape

              4=square shape

              5=heart shape

              6=Diamond shape


Wadannan sune shapes da muke dasu na fuska. Kuma saninsu zai taimakawa mace wajen yin kwalliya kamar inzatai contouring da shafa blush ko jagira yadda zasu fito suyi das a fuska kamar an manna su.


Zaki iya tantance ya shape din fuskarki yake ta hanyar tsayawa cak fuskarki tana kallan mudubi, sai ki samu wani abu dazaki diddiga ajikin mudubin kamr jagira ko maka, kibi shape din fuskartaki ta hanyar diddigawa. To inkin zagaye fuskarki da dige dige ajikn mudubin zakiga yadda shape din fuskarki yake.


 


Bayan kin san kalolin kayan da zasu dace da jikin ki, abu na gaba shine ki san irin shape din jikin ki. Farawa daga fuskar ki domin hatta da kwalliya ana yin ta ne dai-dai da shape din fuskar mutum.

 


TA YAYA ZAN GANE SHAPE DIN FUSKA TA?Muna da shapes na fuska a qalla bakwai zuwa tara. Kama daga Oval, round, diamond, heart shaped da dai sauran su. Zaki gane shape din fuskar Taki ne ta hanya biyu.


Na farko shine ki duba yanayin hair line dinki wato shape din gashin gaban goshin ki.Na biyu kuma shine habar ki (gemu) Sai Ki duba shape dinsa da kyau ki gani sannan ki duba cikin hoton nan ki ga da wanne yafi dacewa. Wannan shine face shape nakiComments