Main menu

Pages

YADDA ZA AYI AMFANI DA KWAI WAJEN GYARAN FUSKA

 


AMFANIN KWAI WAJAN GYARAN FUSKA

Masana sun bayyana muhimmancin amfani da danyen kwai wajan gyaran fata. musamman wajen gyaran fuska, tare da kare fuskar daga matsalar kuraje.


Muhimman amfani guda 5 da ɗanyen ƙwai ke da shi ga fuskar dan Adam;


1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Vitamin


2- Ruwan kwai na rage tsufan fuska


3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje


4- Danyen kwai na kara ma fuska haske


5- Ruwan kai na rage kumburin idanu


Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, 


Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.


Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata Insha Allah.

Comments