Main menu

Pages

MATAR DA TA KOMA NAMIJI TA SO KASHE KANTA SBD ANA KYAMART A



 

Matar da ta koma namiji ta so kashe kanta saboda ana ƙyamarta

Aneera Kabeer ta yi zargin cewa an yi mata sallamar rashin adalci daga makarantar da ta samu aiki bayan watanni biyu



A watan Nuwambar bara, Aneera Kabeer ta halarci jarrabawar neman aiki ta 14 watanni biyu da suka gabata sanye da hula, da kuma takunkumi da ya rufe mata fuska sanye da kayan maza.



Matar mai shekara 35, wadda ta mayar da kanta namiji, ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne sakamakon matsuwar da ta yi biyo bayan irin munanan kalaman da aka sha yi mata a jarrabawar neman aikin baya da ta halarta.



Ta samu aiki na wucin gadi a wata makarantar gwamnati da ke a Jihar Kerala da ke kudancin India - sai dai ta yi zargin cewa an yi mata sallamar rashin adalci daga makarantar bayan watanni biyu.


Shugaban makarantar ya ƙi yarda ya yi magana kan wannan batu. P Krishnan, wanda jami'in gunduma ne, ya bayyana cewa shugaban makarantar ya shaida masa cewa ba a sallami Ms Kabeer ba kuma "ba ta fahimci yadda lamarin yake ba".



Bayan ta rasa yadda za ta yi, sai Ms Kabeer ta je wajen hukumar shari'a ta jihar a watan Janairu -ta bayyana cewa tana buƙatar lauya domin shigar da ƙara kan yunƙurin kashe kai a madadinta.



"Abin da kawai nake so shi ne na yi aiki domin na samu abinci. Sai dai hakan ya ƙi yiwuwa," in ji Ms Kabeer.



Ta karanta littafai da suke nuna yadda mutum zai kashe kansa - sai dai Indiya ta bayar da dama ne kawai a kashe kai ba kai-tsaye ba.



"Na san cewa ba zan bari a amince mani a nan ba. Amma ina so a tura saƙo," in ji ta.



Sai dai tana so ta ja hankalin ƙasar - kuma ta ja hankali na ƙarshe. Gwamnatin cikin sauri ta mayar da martani inda a yanzu ta samu wani aikin.

Comments