Main menu

Pages

SABBIN TSARE TSAREN DA WHATSAPP ZAI KAWO "SOON"

 Manya - manyan Canje - canjen da Whatsapp zai kawo kwanan nan.

Whatsapp dai wata manhaja ce ta tura sakonni kamar yadda kowa ya sani. To akwai Canje - canjen da akai guda 4 da suka shafi groups da zasu fito nan ba dadewa.


Whatsapp dai da kuke gani wadanda ake amfani dashi a Duniya sunfi billion biyu, shiyasa lokaci Zuwa lokaci ake fiddo da update dinsa da ke kunshe da abubuwan da zaisa masu amfani dashi suji dadin shi.


Canji na farko Shine;

Na farko cikin su ya qunshi sabon tsarin wajen yin voice note, Wanda kana cikin yin voice din zaka iya sanya pause, wato dakatawa sannan inkaso Kuma Kai resuming wato ka dora akan wanda ka dakatar ka cigaba da recording.Idan muka koma cikin Whatsapp din wajen website "WABetaInfo" Wannan sabon tsarin zai taimaka ma wadanda ransu ke baci lokacin da suke tsaka da yin voice note sai Kuma kira ya shigo, Wanda hkan kesa dole su sako recording din daga farko, ko kuma suyi shi a yayyanke.

To wannan tsarin zai tai Maka masu wajen pause in sun gama suyi resume.


Bugu da karu, Wannan tsarin zai baka damar sauraro, ko deleting ko cigaba da recording kafin kayi sending.


Sabon Tsari Na biyu;

Whatsapp yana bunkasa sabbin tsare tsaren da zai baku dama kuyi migrating wato kwashe chat history dinku daga android zuwa iOS, haka daga iOS Zuwa android.Sai Sabon Tsari na uku;

Tsari na uku da Whatsapp zai gabatar maku shine ya bunkasa tsarin da zai ba masu amfani da iOS damar react ga duk Wani massage da emoji irin na Facebook messenger app.


 Na Hudu Kuma na karshe shine;

Whatsapp zai bunkasa fannin security, zai zama sai anyi tsarin nan na "two - step verification ga duk masu amfani da Whatsapp.

Comments