Main menu

Pages

KI KOYI YADDA AKE HADA GUMBA DA KANKI


       

        GUMBAR MATA


_Akwai hanyoyi da dama da mata sukebi su hada gumba da kansu saboda muhimmancinta wajen gamsarda oga domin tana karawa mace ni ima kuma tana saka mace taji tana bukatar namiji shiyasa matan Aure da yawa suke sayanta.


Idan kinaso ki hada da kanki ga yanda akeyi zaki samu garin ridi wanda kika soyashi sama sama ko kuma dusar gero ko kuma shi kansa geron shima wanda aka soyashi sama sama kowane daga cikinsu anayi dashi.


Misali idan da dusar gero zakiyi ita dusar zaki hada da mazarkwaila da kanunfari da citta da jar kanwa saiki samu turmi ki zuba amma ki ajiye mazar kwailar saikin daka sauran kin tabbatar sun hadu sosai saiki saka mazar kwailar aciki ki rinka dakawa kada ki saka masa ruwa zakiyi ta dakawa da kansa zai hade musamman idan da ridi kikayi zai hade da kansa sannan ki debeshi ki ajiyeshi. To wannan hadin shine ake kira GUMBAR MATA zaki rinka daukar kadan kina hadawa da madara kinasha idan kuma bakyashan madara kiyi amfanida nono.


Note. Kunsan cewa duk wani sinadari Yana cikin dusar abin shiyasa wasu keyi da dusar gero.
Amma kina iya amfani da geron da ba a surfa ba ki soya shi sama sama sannan ki fara dakawa kamar yadda akai bayani a sama, idan da gero ko Ridi zakiyi duk procedures din daya ne.


A post na gaba zamu kaeo maku ydda ake wata kalar Gumbar Insha Allah.

Comments