Main menu

Pages

GYARAN DA YA KAMATA MATA SUNA YI TUN KAFIN SUYI AURE DA KUMA BAYAN AUREN KARIN NI'IMA A AL'ADANCE A SAWWAKE KUMA A GARGAJIYAN CE. 


 Anaso mace tarinka gyara kanta tun tana gIdan iyayenta basai tayi aure ko kuma tazo yin aure kafin ta fara gyara kanta ba. Wasu da yawan yan mata idan sukaji ance su gyara kansu sai kaga sunayin abin har yana wuce gona da iri. Abun da ya kamata kina yi tun kafin kiyi aure aure shine. 1. TSARKI DA RUWAN ZAFI. Tsarki da ruwan dumi ba karamin taimakawa yakeyi ba wajen gyaran farji. Mata ku kiyaye tsarki da ruwan sanyi sabida ba karamin illa yakeyi ma mace ba. 2. GANYEN MAGARYA. Anaso mace ta dingayin tsarki da ganyen magarya idan da so samune ya zama shine permanent ruwan tsarkin ki shima ba karamin gyara farji yakeyi ba. 3. ZUMA. Anaso mace ta ringa shan zuma chokali daya d safe daya da daddare. Wannan yana taimakawa wajen dawo miki da ni'iman ki da ya fita yayin da kike jinin al'ada. 4. Anaso mace a sa'ilin da take cikin jinin al'adanta ta rinka shan zuma chokali uku kullum da safe har tsawon kwanakin da zata gama al'adan ta. 5. A sa'ilin da kika gama al'ada bayan kinyi wanka sai ki dan debi zuma kadan da hannun ki ki saka a bakin farjinki anaso kiyi hakan har na tsawon kwana uku. 6. MAN HABBATUS SAUDA. Zaki samu man habbatus sauda shima kirinka sha kina shafawa a farjinki. 7 KANKANA DA MADARA. Anaso mace ta rinka shan kankana da madara a ko wani lokacin da ta gama al'adan ta. 8. KANKANA DA CUCUMBER. zaki yanka kankana da cucumber sai ki hadasu kiyi blending kirinka sha duk lokacin da kika samu halin yi. 9. MISKIL A'ISHA. Anaso mace ta samu miskil Aisha ki rinka sa kadan a farjinki. Zakiji koda kin wanke pants dinki wannan kamshin yana nan a jikin shi. Wadan nan abubuwan dana lissafa suna da yawa irin wanda ya kama mace ta rinka yi kenan tun tana gaban iyayen ta. Da Allah mata a daina yawa chushe chushe ma farji yawan yin hakan ba karamin matsala yake jawo wa ba....


       

Comments