Main menu

Pages

KINA SO KI ZAUNA DA MIJINKI LAFIA, TO KI RIKE WANNAN SIRRIN


 KI RIKE WANNAN SIRRIKAN DOMIN KI ZAUNA DA MIJINKI LAFIYA


Amman sai kin sa juriya da hakuri👌🏼👌🏼


(1) Ki guji binciken wayar mijinki kada ki rinka daukan wayarsa ba tare da izininsa ba, domin dai ko ba komai yan magana suna cewa kazantar da baka gani ba tsafta ce.(2) Ki guji yin zargi akan mijinki na neman mata ki sa zuciyanki kowane lokaci mijinki na da daman kara aure tunda addini bai hana masa ba, madadin ki ta bin diddiginsa yana Neman mata kidage da yi masa addu'a domin samun kariya daga fadawa yin Zina.(3) Ki daina yawan sa ido👀 da bin diddigi me mijinki yake yi domin da yawa daga cikin maza sanya musu ido a kan duk wata harka tasu tana kawo matsala tsakanin miji da mata.(4) Kiguji yawan korafi anyi min wannan gobe anyimiki kaza kada ki kasance mace mai yawan fushi a gun mijinki ki rinka bari sai anyi miki laifi kin tara sannan sai ki fada kuma shima ba a cikin gadara zaki fada ba.(5) Kiguji hana mijinki saduwa da ke domin kun samu sabani, hakan babban kuskure ne da zai ji ya tsani yi da ke ko da kuwa lokacin Baku samu sabani ba hakan sai ya sanya sha'awarki ta fita daga cikin zuciyarsa.

Comments